Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Wani fitaccen ɗan kasuwa a fannin sayar da tsire a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Yusuf Kunya, ya bayyana cewa ma’aikatan da ke cikin tukubar tsire ta Rahusa Suya, sun fi yawancin ma’aikatan gwamnati samun garabasa da walwala ta fuskar albashi, lafiya, da jin daɗin rayuwa.
Alhaji Abdullahi, wanda shi ne Manajan Rahusa Suya, kuma ɗan marigayi Sarkin Fawar Kunya na ƙaramar hukumar Minjibir, ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a kasuwar Dimawa da ke Kano, inda ya ce sana’ar tsire ta zama wata babbar hanyar samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata.
A cewarsa, a kullum ana sayar da tsinken tsire sama da dubu ɗaya (1,000), tare da yankan shanu biyu, wanda hakan ke baiwa mutane akalla 40 aikin yi a rana ɗaya. Ya bayyana cewa tsire daga lokacin da ake yanka nama har zuwa lokacin da ya isa hannun mai siya, tana wucewa ta matakai daban-daban da ke samar da ayyuka masu yawa.
“Yanzu muna da ma’aikata na dindindin guda 25, kuma kowane ɗaya yana da mutane kusan biyar da yake dogara da shi a kullum. Akwai masu yankan nama, masu saka tsinken tsire, masu hada kayan yaji, masu gasa nama, da masu sayarwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa akwai ma’aikatan da suke samun N5,000 kullum, wanda idan aka tara a wata yana kaiwa N150,000, baya ga abincin su, kula da lafiyarsu, da sauran tallafi. Haka kuma akwai mata fiye da 20 da ke aiki a sashen gurasa da sauran kayayyakin haɗin tsire, waɗanda su ma ke amfana da wannan sana’a ta halal.
Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa sana’ar tsire ta fi yawancin ayyukan gwamnati albarka da walwala, saboda tana da ’yanci, halalci, da biyan buƙatun rayuwa. “A yanzu ba zan iya aikin gwamnati ba, domin wannan sana’a ta tsire ta ishe ni da abin dogaro kuma tana kawo mini kwanciyar hankali,” inji shi.
Ya ce yana alfahari da kasancewarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka gaji wannan sana’a daga mahaifinsu, yana kuma fatan ’ya’yansa da jikokinsa su ci gaba da riƙe wannan sana’a mai daraja da mutunci.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ƙirƙiri makarantar koyon sana’ar fawa, domin koyar da matasa dabarun sarrafa nama da kiwon kaji a matsayin hanyar rage zaman banza da samar da ayyukan yi.
A cewarsa, “tunda akwai makarantu na koyon sana’o’i irin su fina-finai, kwallon kafa, da kiwon kaji, ya dace a samu makarantar koyon sana’ar tsire. Wannan sana’a ta gado ce daga kakanni, kuma tana taimaka wa tattalin arzikin jama’a da na jiha.”
