Masu neman a kafa ƙasar Yarabawa wawaye ne, cewar Aregbesola

Daga UMAR M. GOMBE

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana masu rajin kafa ƙasar Yarabawa da magoya bayansu a matsayin wawaye.

Aregbesola ya bayyana haka ne a wajen  taron bikin cikarsa shekara 64 da haihuwa wanda aka gudanar a Zenabab Hotel da ke Ilesha, jihar Osun a Asabar da ta gabata.

Ministan ya gargaɗi masu wannan ƙudiri da su yi la’akari da yara ƙanana da mata da tsofoffi da masu fama da nakasa da ake da su a yankin.

Ya ce Nijeriya ita ce ƙasar da za ta cire wa yankin Afirka kitse a wuta daga kowane irin nau’i na danniya, don haka ya ce Nijeriya ba za ta yarda da ra’ayin ɓallewa daga gare ta ba.

A cewarsa, “Duk wani abu da ka iya zama barazana da kuma matsala ga Nijeriya, hakan zai haifar da koma-baya ga ƙasarmu na tsawon shekaru 50.”

Wasu sassan Nijeriya, musamman yankin kudancin ƙasar, na ra’ayin ɓallewa daga Nijeriya sannan ya zama ƙasa mai cin gashin kanta, shi ne zai kawo ƙarshen matsalolin da yankin ke fama da su.