Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Hana Fataucin Bil’adama ta ƙasa (NAPTIP) ta bankaɗo sabbin hanyoyin da masu safarar mutane ke amfani da su wajen yaudara da gallaza wa ’yan Nijeriya musamman matasa da mata.
Da ta ke magana a Abuja a wani taron manema labarai na bikin Ranar Yaƙi da Fataucin Bil Adama ta duniya na shekarar 2025, Shugabar Hukumar NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta yi gargaɗin cewa a yanzu masu fataucin na yin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani, bayar da tallafin karatu na bogi, tsarin lamuni ta yanar gizo, har ma da masana’antar jarirai don kama mutane.
“Yaƙin da ake yi da fataucin bil’adama yana tasowa tare da sabbin abubuwa masu tayar da hankali, a kowace rana, masu fataucin su na ƙirƙiro sabbin dabaru don yaudarar masu rauni,” inji ta.
Bikin, mai taken “Fataucin Mutane Aiki Ne Ake Tsarawa – A Kawo ƙarshen Sa”, ya ba da haske game da ƙaruwar laifukan ta’addanci ta yanar gizo.
A cewar NAPTIP, daga cikin nau’o’in ɗaukar ma’aikata da masu fataucin su ke amfani da su cikin sauri sun haɗa da: Bayar da aikin yi na jabu da tallafin karatu a ƙasashen waje, tsarin lamuni na yanar gizo inda masu safarar su ke neman ƙaruwanci a matsayin hanyar biyan bashin da kuma ɗaukar aikin ’yan Yahoo a faɗin Nijeriya, Ghana da sauran ƙasashen yammacin Afirka.
Domin yaƙar ƙaruwar fataucin mutane, NAPTIP ta haɓaka ƙarfin jami’anta na Intanet don sa ido, ganowa, da kuma rufe dandalolin ɗaukar ma’aikata na bogi.
“Za mu inganta dabarun mu da kuma ƙara haɗin gwiwa da sauran hukumomi domin daƙile masu fataucin,” inji ta.
“A cikin watanni masu zuwa, masu fataucin mutane za su ga cewa Nijeriya ta kasance ƙasa mai tsananin gaba da fataucin mutane.”
Ta kuma jaddada buƙatar masu hannu da shuni, da ƙungiyoyin farar hula, da cibiyoyin gargajiya su haɗa kai wajen kare ‘yan Nijeriya, musamman a yankuna masu rauni da kuma kan iyakokin ƙasar inda matsalar ta fi ƙamari.
“Mu ajiye hamayya a gefe, mu yi aiki tare, lokaci ya yi da za a kori masu safarar mutane daga Nijeriya har abada,” inji ta.
Shima da yake jawabi a wajen taron, Cheikh Toure, wakilin ƙasar na ofishin Majalisar ɗinkin Duniya mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka (UNODC), ya sake jaddada aniyar Majalisar ɗinkin Duniya na taimaka wa Nijeriya wajen wargaza hanyoyin safarar mutane.
