Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Nijeriya na shirin fara amfani da fasahohi irin – ƙirƙirarriyar basira ta AI, geospatial analytics, da bayanan tauraron ɗan adam domin magance ƙarancin abinci a ƙasar da kuma sa ido kan yadda ake noman abinci, haɗa manoma da kasuwa, da kuma rage asarar bayan girbi.
Shettima ya bayyana haka ne a wajen buɗe taron hada-hadar hannayen jari na tsarin samar da abinci ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNFSS+4), a Addis Ababa, ranar Litinin.
Taron na da nufin samar da makoma mai ɗorewa wadda ke ginuwa kan yalwa, daidaito da mutuncin ɗan’adam.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce abinci mai gina jiki a yanzu ya kasance ginshiƙin tsarin ci gaban ƙasa daga 2021 zuwa 2025 da kuma ajandar Nijeriya har 2050.
Shettima ya ce: “Juyin juya halin masana’antu na huɗu ba wai kawai ya kawo cikas ga tsohon tsarin ba ne, amma ya ba mu kyautar kayan ƙida waɗanda a da suka keɓanta da tunani.
Shettima ya ce, Nijeriya ta ƙara saka hannun jari a shirye-shiryen ciyar da makarantu, noma mai kula da abinci mai gina jiki, da wayar da kan al’umma.
A cewarsa, ta hanyar shirin ‘Nutrition 774’, gwamnati na sanya dukkanin ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya a cibiyar samar da abinci mai gina jiki.
Ya ce, “A yin haka, muna samar da ci gaba mai ɗorewa a cikin gida. Muna canja tabbatar da wadatar abinci.”
Shettima ya bayyana cewa, Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da shirin samar da abinci da abinci mai gina jiki mai ɓangarori da yawa na ƙasa don zama ɓangaren aiwatar da manufofin abinci a ƙasa.
Ya ƙara da cewa, gwamnati ta bayar da umarnin kafa sassan samar da abinci a ma’aikatun da abin ya shafa.
A cewarsa, waɗannan su ne ginshiƙan sake fasalin hukumomi da kuma gine-ginen sarrafa abinci mai gina jiki.
Shettima ya ce, “Wannan ya wuce taron koli, wannan hisabi ne, duniya tana canjawa a idanunmu.
“Dole ne mu yi aiki, kuma mu yi shi tare.
A cewarsa, dole ne a gina shi da haƙuri da juriya, tare da jajircewa da tunani da tsare-tsare mai kyau, tare da azama wajen ɗaukar nauyi.
Shettima ya tabbatar da cewa Nijeriya a shirye ta ke ta saurare, koyo da jagoranci a duk inda ake buƙatar shugabanci.
