Mata a Zamfara sun nuna goyon bayansu ga Marafa a ƙarƙashin NDC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Dubban mata daga ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara sun gudanar da gangami domin bayyana goyon bayansu ga Sanata Kabir Garba Marafa a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

An gudanar da taron ne a Gusau, babban birnin jihar, domin ƙaddamar da ƙungiyar Marafa Amazons for Change, wadda Modibbo Aminu ya kafa.

Marafa Amazons for Change ƙungiya ce da ta ƙunshi matasa mata, masu ilimi da ’yan kasuwa, waɗanda suka haɗa kai da manufa guda ta ceto Jihar Zamfara da samar da sabon shugabanci a shekarar 2027.

Da take jawabi a wajen taron, shugabar ƙungiyar matan, Hajiya Sadiya Salisu, ta bayyana gwamnatin Gwamna Dauda Lawal a matsayin wadda ta gaza, musamman wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Ta koka da cewa mata da dama sun zama zawarawa sakamakon rashin tsaro, yayin da mazajensu da ’yan uwansu suka zama mabarata sakamakon ayyukan ’yan bindiga.

Hajiya Sadiya ta bayyana cewa zaɓen Sanata Kabir Garba Marafa ya zama wajibi a gare su, tana mai alwashin ci gaba da wayar da kan al’umma daga tushe domin tabbatar da nasarar sanatan.

Taron, wanda aka gudanar cikin lumana, ya samu halartar mata da ’yan mata da dama, waɗanda suka bayyana aniyarsu ta bayar da gudummawa wajen kayar da gwamnatin yanzu.

Hajiya Sadiya ta sake bayyana gwamnatin Dauda Lawal a matsayin wadda ta gaza tabbatar da makomar ’yan Zamfara, tana mai alƙawarin cewa ƙungiyar za ta yi amfani da ƙuri’unsu wajen sauya gwamnati a zaɓe mai zuwa.

“Za mu wayar da kai daga gida zuwa gida, daga mazaba zuwa mazaba, daga kasuwa zuwa kasuwa, har sai Marafa ya zama gwamna,” inji Hajiya Sadiya.

A cewarta, kasancewar Modibbo Aminu ya samu nasarar kafa ƙungiyoyi biyu masu ƙarfi, wato Marafa Ambassadors for Change da Marafa Amazons for Change, hakan ya nuna ƙwarewarsa wajen jagoranci da haɗa kan masu ilimi a faɗin jihar.

Ta ce ƙungiyoyin biyu suna da ƙarfin da za su iya kai Sanata Kabir Garba Marafa ga kujerar gwamnan Zamfara a 2027.

ƙungiyar ta kuma yaba da gudummawar Abba Garba, tana mai cewa ƙoƙarinsa a wannan tafiya ba za a iya misalta shi ba.

Hajiya Sadiya ta yi kira ga dukkan masu ilimi da mata masu kishin jihar da su shiga wannan tafiya, wadda ta bayyana a matsayin tafiyar da za ta yi wa kowa adalci.

Ta ce Marafa Ambassadors for Change da Marafa Amazons for Change ba ƙungiyoyi ne na yau da kullum ba, illa manyan ƙungiyoyi masu ilimi, tsari da shirye-shiryen da suke ganin za su taimaka wajen ceto Jihar Zamfara.

A cewarta, Sanata Marafa shi ne ɗan siyasa guda a Zamfara da ke da gaskiya, ƙwazo da hangen nesa, kuma shugaba ne wanda ba ya karya, yaudara ko cin amanar al’ummarsa.

By ukarofi

Leave a Reply