Matatar Ɗangote ta ƙara farashin fetur zuwa N799

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matatar Man Fetur ta Ɗangote ta sanar da ƙarin farashin lita daga N699 zusa N799.

A saboda haka ne gidajen man MRS Oil suka fara sayerwa akan N839 a sassan Nijeriya.

Ƙarin farashin ya biyo bayan ƙarewar tallafin wucin-gadi na rangwamen farashi da matatar ta samar a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara, kamar yadda wata sanarwa da ta aike wa NewsPointNigeria a ranar Litinin ta bayyana.

An samar da rangwamen ne domin rage wa al’ummar Nijeriya nauyin kashe kuɗi a lokacin da buƙatun man fetur ke ƙaruwa sakamakon tafiye-tafiye da sauran hidimomin bukukuwa.

Majiyoyi sun bayyana cewa matatar ta yanke wannan mataki ne bisa la’akari da canjin farashin kayayyakin samar da mai, farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma tsadar jigila, lamarin da ya sa ba za a iya cigaba da hada-hadarsa akan rangwamen ba.

Kamfanin ya jaddada aniyarsa ta cigaba da yunƙurin aiwatar da matakan ɗorewar kasuwa da samar da fetur ba ƙauƙautawa a faɗin Nijeriya.

Wannan matakin janyo ce-ce-ku-ce game da tasirin sauye-sauyen farashin man fetur ga tattalin arzikin ƙasa da rayuwar talakawa musamman ganin yadda al’umma ke fuskantar matsin gudanar da yau da kullum.

By Babaji