Daga AISHA ASAS
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Masu Shirya fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN) dake Arewa ta bayyana matuƙar alhini da jimami bisa mummunan kisan gillar da aka yi wa wata uwa da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranci da ke birnin Kano, lamarin da ya girgiza zukatan al’umma baki ɗaya.
A wata sanarwar ta’aziyya da Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Shehu Hassan Kano, ya rattaba wa hannu, MOPPAN ta miƙa sakon jaje da tausayawa ga Gwamnatin Jihar Kano, ɗaukacin al’ummar jihar, da kuma iyalan mamatan, musamman Malam Haruna, mijin matar da aka kashe.
Sanarwar ta bayyana cewa, wannan lamari na tayar da hankali da zubar da jinin bayin Allah ba tare da laifi ba, ya bar ƙungiyar cikin tsananin firgici da baƙin ciki. Ta ce, rasa rayukan uwa guda ɗaya da ’ya’ya shida musamman yara marasa laifi, bala’i ne da kalmomi kaɗai ba za su iya misalta girman raɗaɗinsa ba.
MOPPAN ta jaddada cewa, wannan mummunan lamari ba rauni ne ga iyali kaɗai ba, illa harin kai tsaye ne ga lamirin al’umma da mutuncin ƙasa baki ɗaya. Saboda haka, ƙungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnatin Jihar Kano da jami’an tsaro, tare da yaba wa ƙoƙarin da ake yi wajen bincike da neman gaskiya.
ƙungiyar ta kuma yi kira da a tabbatar da adalci ya yi tasiri, ta yadda za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika, tare da ƙarfafa matakan kariya domin hana faruwar irin wannan masifa a nan gaba.
Ga Malam Haruna, MOPPAN ta miƙa sakon ta’aziyya ta musamman, tana bayyana cewa asarar matar aure da ’ya’ya a lokaci guda abin tausayi ne da ba zai taɓa mantawa ba. ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya ba shi juriyar zuciya, haƙuri da ƙarfin gwiwa don jure wannan babban rashi.
Haka zalika, ta roƙi Allah (SWT) Ya gafarta wa mamatan, Ya karɓi baƙuncinsu Ya sanya su a Aljannar Firdausi, Ya kuma kwantar da hankulan iyalansu da al’ummar Jihar Kano bakiɗaya.
Sanarwar ta ƙare da tabbatar da girmamawa da cikakken tausayawa daga shugabanni da mambobin MOPPAN ga duk waɗanda wannan masifa ta shafa.
