Ku daina yin kuɗin goro kan harkar fim babu tarbiyya – Maryam Salisu

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Sabuwar jaruma a masana’antar Kannywood Maryam Salisu ta fito shirin ta na zama babbar jarumar da kowa zai yi maraba da ita da zarar ta samu damar da za ta bajekolin basirar ta a cikin harkar ta Kannywood.

Babu shakka idan har Maryam Salisu ta samu damar da take so ta samu na ɗaurin gindi daga masu juya harkar masana’antar, to ba abin mamaki ba ne cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta kai ga matakin da kowa zai san da ita. Ba don komai ba kuwa sai don yadda Maryam Salisu ta kasance yarinya mai sauƙin kai da kuma girmama na gaba. Kuma daidai gwargwado tana da ilimi da kuma tarbiyya. Sannan duk wata siffa ta kyaun sura da mata suke ji da ita, Maryam Salisu za a iya saka ta a cikin kyawawan mata.

A cikin wata tattaunawa da muka yi da ita, sabuwar jarumar ta yi mana bayanin dalilin ta na shiga harkar fim, burin da take da shi da kuma sauran batutuwa da suka shafi rayuwarta. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar tamu ta kasance.

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatun mu.

JARUMA MARYAM: To Assalamu alaikum, da farko ni dai sunana Maryam Salisu kuma an haife ni ne a garin Jos a yanzu ina da shekara 23, na yi karatun firamare da sakandare duk a garin Jos. Bayan na kammala karatu da ɗan wani lokaci sai na dawo Kano a yanzu ina zaune a garin Kano, kuma ina aiki ko sana’a ta harkar gyaran jiki wanda a yanzu shi ne abin da na fi kwarewa da shi a matsayin sana’ar da nake yi.

Ki na ɗaya daga cikin sabbin jarumai da suka shiga harkar fim a wannan lokacin. Ko me ya ba ki sha’awar shiga harkar fim ɗin a wannan lokacin?

To gaskiya daman ba a wannan lokacin ne na fara sha’awar na yi harkar fim ɗin ba. Ina da sha’awa ta shiga harkar tun ina ƙarama, amma da yake ina karatu , kuma ga ni karama a lokacin na san ko da na so na shiga ba za a bar ni ba a gida. Don haka sai na bari zuwa lokacin da zan kammala karatun domin hakan zai fi mini sauki. A yanzu da na kammala karutu kuma ga shi ina garin Kano da zama wadda ita ce cibiyar harkar fim ɗin, sai na ga ya kamata na gwada neman damar da zan ce cika burina na zama jaruma a cikin masana’antar Kannywood. Kuma a yanzu Alhamdulillah, ina ganin buƙatar da nake da ita za ta biya saboda alaƙar da nake ta samu da ‘yan fim da a kullum muke tare da su.

Duk lokacin da mace za ta shiga harkar fim ta na samun matsala a gida ko a cikin kawayen ta saboda za su rinƙa cewa saboda me za ta shiga harkar fim. Ko kin samu irin wannan maganar daga gida ko ƙawaye?

To gaskiya ni ban samu hakan ba. Saboda ko a baya don ina karatu ne sai na ga a wannan lokacin iyayena ba za su bar ni ba, amma da na gama sakandare ban samu matsala ba, kuma ta ɓangaren kawaye ma ai wannan ba ta taso ba saboda kowa yana nemar wa kansa mafita ne tun da a yanzu na girma na mallaki hankalina ai ina da damar da zan gane abu mai kyau da wanda ba shi da kyau. A yanzu iyayena su ne za su ce na yi ko kada na yi, saboda a ƙarƙashin su nake, su kuma sun bani damar na yi, to ai ka ga ba ni da matsala.

A yanzu da kika shigo cikin ‘yan fim, ya kike ganin yadda suke rayuwa?

Gaskiya na ga yadda suke rayuwar su tana burge ni, domin duk yadda ake maganar su da na haɗu da su sai na ga ba haka suke ba. Ana mu’amala ta mutunci ga girmama juna da yawa da na haɗu da su sun nuna mini kauna, don haka suna da kirki da ƙaunar junan su 

Baya ga harkar gyaran jiki ko akwai wani abu da kika fi kwarewa?

E ina da kwarewa a harkar tallace-tallace wanda nake yi wa kamfanoni kuma gaskiya na kware sosai. domin muna yi wa kamfanoni da dama talla, kuma a yanzu ina kan yi duk wani kamfani da yake son na yi masa talla na kayansa ƙofa a buɗe take a wajena.

Harkar fim a wajen ki sha’awa ce ko kuma wani buri kike so ki cika?

Gaskiya harkar fim a wajena ta fi karfin sha’awa, domin zan yi fim ne a matsayin sana’a wadda zan yi amfani da ita wajen rufawa kaina asiri tare da kiyaye mutunci na, domin a yanzu sana’ar ka mutuncin ka don haka harkar fim sana’a na ɗauke ta ina fatan kuma na samu damar da zan zama babbar jarumar da zan cika burina. Kuma ko da ina son na yi suna a cikin harkar fim, ai sai na karɓu na yi sunan zan samu cikar burina. To ina fatan Allah ya bani damar da zan kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman da za su taka rawar gani a cikin harkar fim.

To ko kin fara ganin alamar cikar burin naki zuwa yanzu?

Haka ne na fara ganin hakan, domin a yanzu ma akwai wasu ayyuka da na samu ba ɗaya ba biyu ba, waɗanda za a fara aikin a nan gaba kadan. Kuma abin da ya ba ni mamaki duk manyan fina-finai ne waɗanda ina sa ran in sha Allahu za su fito da ni a matsayin ɗaya daga cikin jaruman da za a kalla a sabuwar shekarar nan ta 2026. Don ni kamar yadda na faɗa maka ina son na kai matakin da zan zama babbar jaruma ne, don ta haka ne zan samu cikar damar da nake so na taimaka wa na kusa da ni da ma waɗanda suke nesa suke buƙatar taimako. Idan son samu ne ma ina son na kasance ɗaya daga cikin fitattun mata da suke taimakawa al’umma ta ɓangarori daban daban. Saboda ni dai da ka ganni ina da tausayin na ga wani yana cikin yanayi na buƙatar taimako, don haka na kan yi daidai karfina, to ina son na samu damar da zan rinƙa taimaka wa masu buƙatar taimako, wannan shi ne cikar burina.

Harkar fim ana kallon sai mutum yana da ɗaurin gindi yake samun shiga ke da kika shigo harkar ya kika gani?

Ni dai Alhamdulillah gata na Allah, kuma ɗaurin gindi na Allah, don haka ina da karfin gwiwar zan yi nasara a kan abin da na saka a gaba kuma ba na shakka ko fargaba, da ƙarfin ikon Allah zan yi nasara.

Yanzu idan za a ce ki bada shawara ga masu harkar fim, to wacce shawara za ki ba su?

Ni kawai abin da nake gani da dan fim da wanda ba dan fim ba, duk inda mutum ya samu kansa, to ya yi ƙoƙarin kiyaye mutuncin sa, kuma mutane su gane ita fa rashin tarbiyya tun daga gida ake samun ta, babu yadda za a yi mutane su taso ba su da tarbiyya tun daga gidansu su zo suna rashin tarbiyya a fim kuma a ɗauka sai da suka shiga harkar fim suka samu rashin tarbiyya. To ni dai Alhamdulillah, na samu tarbiyya a gidanmu, don haka nake alfahari da kasancewar na tashi a gidan tarbiyya, saboda haka mutane su daina yin kuɗin goro suna cewa harkar fim babu tarbiyya a cikin ta. Kowace sana’a akwai masu tarbiyya akwai marasa tarbiyya, ya danganta ga yadda mutum ya tashi a gidansu, ina fatan mutane za su rinƙa yin adalci a cikin maganganu su.

To madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.

By ukarofi