Matsalar tsaro: Gwamna Raɗɗa ya gana da sarakunan Katsina da Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya gudanar da wani muhimmin taro da Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, da Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, tare da hakimai da dagatai masu unguwanni daga sassa daban-daban na faɗin jihar.

Taron ya haɗa manyan shugabannin na masarautun gargajiya domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi mulki, ci gaban al’umma uwa uba matsalar tsaro tare da mai da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masarautun gargajiya.

Gwamnan ya bayana muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ƙarfafa haɗin kai, da kuma tallafa wa shirye-shiryen gwamnati a matakin ƙasa da ƙasa (grassroots).

Taron ya samu halartar kakakin majalisar dokokin Jihar Katsina, Nasir Yahya Daura; babban alƙalin jihar, Mai shari’a Musa Ɗanladi Abubakar; shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Abdulkadir Mamman Nasir da sauran yan majalisar zartarwa ta Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply