Matsaya ta kan cecekucen karrama Rarara – Farfesa Abdalla

Spread the love

Ana ta cecekuce kan matsayata game da zuwa taron nazarin waƙoƙin Rarara.
Na ga yadda na yamutsa hazo a kan ƙudirin ƙaddamar da gagarumin taro na nazarce-nazarcen waƙoƙin Dauda Kahutu Rarara.

A sanarwar farko, cewa aka yi ni ne Baƙo Mai Babban Jawabi. Na ce ni ban san da maganar ba – hasali ma mutane ne suka riƙa aiko min da sanarwar domin tabbatar da ita. Da ya ke ba wani sahihin bayani da zan bayar, na ƙaryata shigata cikin lamarin.

Daga baya Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, Katsina (FUDMA) inda aka ce za a yi taron, ta fito ta ce yadda aka sanar ba haka bane, ta kuma ba da haƙuri.

Amma sai ga shi mabiyan Rarara sun kwararo a wurare da dama suna cewa hassada na ke yi masa. Wani ma cewa ya yi idan da Rarara zai aiko min da kuɗi da aguje zan je taron. Duk waɗannan kwamentocin sun daɗa haskaka irin tunanin da yawa daga cikin mabiyan Rarara, ko da shi ba shi da irin nasu tunanin.

Don kaɗai na ce ba a sanar da ni biki ba, saboda haka ba zan je ba, sai a ce ina yi wa mai bikin hassada?

Ai ban ce kada a yi ba, kuma ban ce in bana ciki abin ba zai yiwu ba. Ban kuma banzatar da bukatar a yi haka ba. Hasali ma kafin da yawa daga cikin waɗanda za su gabatar da maƙala, ni na yi nawa rubutun wanda na kira “Rarara’s Invective Barbs: Innuendoes, Body Shaming, and Political Lyrics in Kano.” Waƙoƙi 29 na ɗauka wandan da suka yi magana a kan siyasar Kano (da kuma ɗaya ta siyasar Katsina). Da na kai shakuka 60 sai na tsaya – domin kullum na ce zan tsaya, sai ya yi wata waƙa ta buƙaci a ci gaba! Saboda haka menene abin hassada a cewa kamata ya yi a bi kyakkyawan tsari in za a shirya taro mai muhimmanci irin wannan?

Sannan ai kusan manyan mawaƙan Hausa duk an yi taro a kan su. Ba wani cece-ku-ce. Ko mutum ba ya son waƙoƙin Rarara (ko ma shi kan sa Rarara ɗin), dole ya yarda dai ƴan siyasar da ludayinsu ke kan dawo na ji da shi – domin shi kaɗai ne mawaƙi (ko maroƙi a wani ƙaulin) da duniya ta ga Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tashi ya gaishe shi a wani taro. To ai kaga kafasiti ya kai kafasiti.

Karrama mawaƙa waƙan da za a ga kamar waƙoƙin su shirme ne, ba sabon abu bane. Manyan jamio’o’i na duniya na yin haka. Misali, Harvard University harma kuɗi ta gindaya saboda karrama waƙoƙin Nasir Jones (NAS) mawaƙin Rap a Amurka. Ga fassarar ChatGPT a kan manufar wannan yunƙurin:

“A tsawon aikin sa na fasaha, Nas ya kasance alama ta neman kyakkyawan sakamako ta hanyar haɗa ƙwarewar fasaha, tsokacin al’umma, da ƙirƙira, yayin da yake bayyana kuma yana wakiltar kalubalen rayuwa iri-iri. Manufar tallafin (Fellowship) ita ce taimakawa da ƙarfafa bincike da fahimta game da ilimi, fasaha, al’adu da jagoranci, ta hanyar musayar masu fasaha da masana da ke zaune a Cibiyar Binciken Du Bois. Tallafin Nasir Jones Hiphop shi ne na farko a cikin tarihin ilimi da aka sanya sunan wani mawakin hiphop a kansa.”

Saboda haka ba manazarcin da inda ya kai kafasiti da zai ƙullaci wani yunƙurin bunƙasar fahimtarmu game da abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummatan mu.

Shi ya sa za mu nazarci su Murja Kunya, Hassan Makeup, Blackky Man Funtuwa, Ƴan Daudu, Malamai, kai idan ma wani mahaukacin ya ɓullo, sai a buga da shi.

A ƙarshe, kyayyakyawar alaƙa ce tsakanina da Rarara. Mun haɗu ya girmama ni sosai, har hoto muka ɗauka. Saboda haka masu mutuwa su mutu!

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya wallafa ne a shafinsa na Facebook

By Babaji