Matsin tattalin arziƙi da tsadar gidaje na hana matasa yin aure a Nijeriya — UNFPA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNFPA), ta ce matsin tattalin arziƙi da tsadar gidaje na sa matasa da dama a Nijeriya jinkirta yin aure.

Wakiliyar UNFPA a Nijeriya, Muriel Mafiko ce, ta bayyana hakan yayin jawabi a wajen bikin Ranar Yawan Jama’a ta Duniya ta 2026.

Ta ce wani bincike da hukumar ta gudanar ya nuna cewa yawancin matasa har yanzu suna son yin aure da kuma haihuwar yara.

Sai dai rashin aikin yi, yarancin samun kuɗi, tsadar gidaje, rashin tsaro, da yarancin samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya na hana su cimma wannan buri.

Ta bayyana cewa waɗannan matsaloli na sa matasa su kasa tsara makomarsu cikin ƙwarin gwiwa.

A cewarta, mutane da dama na tunanin matasan yau ba sa sha’awar aure ko samar da iyali, amma sakamakon binciken ya nuna akasin haka.

Yawancin waɗanda aka tattauna da su sun ce suna son yin aure, kuma suna da burin haihuwar yara biyu.

Duk da haka, suna fargabar ko za su iya samun gida da kuma kula da iyalinsu.

Mafiko, ta ce ya kamata gwamnati ta tallafa wa matasa ta hanyar zuba jari a fannin kiwon lafiya, shirye-shiryen tallafa wa iyalai, tazarar haihuwa, kula da yara, da sauran manufofin da za su ba su damar gina rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

Ta ƙara da cewa matasan Nijeriya na daga cikin manyan arziyin yasar, kuma idan aka ba su ilimi, ƙwarewa da damar ci gaba, za su iya samar wa kansu kyakkyawar makoma.

Shi ma Shugaban Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta yasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar Nijeriya ’yan ƙasa da shekara 30 ne.

Ya ce wannan yawan matasa babbar dama ce wajen yiryire-yiryire, kasuwanci, ci gaban fasaha da bunƙasar tattalin arziyi.

Sai dai ya jaddada cewa hakan ba zai tabbata ba sai an samar wa matasa ingantattun damammaki da goyon baya.

By ukarofi

Leave a Reply