
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Za’a gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, inda manyan mahlarta taron suka haɗa da ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Muhammed wanda shi ne shugaban taron da shugaban hukumar hana fatauci da miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Janar Buba Marwa Mai ritaya da wanda ya ƙirƙiri cibiyar kimiyyar ‘Data’ ta ƙasa, Dakta Bayo Adekanbi da kuma babban sakataren ofishin kula da kuɗaɗen makarantun gaba da sekadire, ‘ARC.’ Sonny Echono da sauran su.
Hukumar kula da harkokin tallace-tallace ta ƙasa (ARCON) ta shirya taron inda shugaban NDLEA, Buba Marwa zai zama babban baƙo wanda za a yi na kwana ɗaya.
Shugaban shirye-shiryen taron, Farfesa Rotimi Olatunji ya bayyana wa manema labarai cewa taron ya ƙunshi tattaunawa da wakilai daban-daban kan muhimman abubuwan da suka shafi talla da kuma ƙaddamar da rubutaccen littafin harkokin tallace-tallace da kasuwanci wanda ARCON ta wallafa.
Za kuma a gabatar da gasar talla daga wakilan manyan makarantu da aka zaɓo daga shiyyoyi guda shida na ƙasar nan.
Daraktan ARCON, Dakta Olalekan Fadolapo, ya ce taron zai bada damanmaki ga al’umma wajen amfani da salo daban-daban na kimiyya da fasaha a harkokin tallace-tallace a matakai da dama wajen bunƙasa harkar a Najeriya.
