Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Juma’a Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ta yi murabus daga muƙaminta na minista.

Hakan na zuwa ne bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar ga masu niyyar tsayawa takara a 2027 da ke riƙe da muƙaman gwamnati na su ajiye domin su mayar da hankali akan abu ɗaya.

Ta sanar da murabus ɗin nata ne a wani rubutu da ta wallafa ta shafukan sada zumunta, inda ta gode wa shugaban ƙasa da ɗaukacin ’yan Nijeriya bisa damar da aka ba ta.

Onyejeocha, ta ce ta ɗauki aikin a matsayin babban gata, tare da yaba wa ma’aikatan ma’aikatar bisa gudunmawar da suka bayar wajen inganta haƙƙin ma’aikata da samar da ayyukan yi acikin al’umma.

Ta zama mutum ta uku cikin ministocin da suka ajiye muƙamansu domin shirin shiga zaɓen 2027, inda a ‘yan kwanakin nan ne Sa’id Alƙali da Yusuf Tuggar suka ajiye aikin minista a ma’aikatun sufuri da na harkokin waje domin shiga takarar gwamna a jihohin Gombe da Bauchi.

By Babaji