Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun hari shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin Jihar Zamfara, Alhaji Muktar Lugga, kwanton ɓauna, yanayin da ya tsallake tsira da kyar daga harin a babbar hanyar Funtua zuwa Gusau kusa da ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe.
Rahotanni sunyi nuni da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:16 na yamma a ranar Alhamis yayin da Hon. Muktar Lugga ke dawowa zuwa Gusau tare da direbansa da wasu mutane biyu.
Rahoton ya nuna cewa ‘yan bindigar sun fito daga ɓangarori biyu na titin, suna harbin motar Lugga.
Majiyar mu ta tattaro cewar a yayin harin harsashi ya ratsa gilashin motar, kuma wani mahari na biyu ya yi yinƙurin harbi amma makaminsa ya tsaya cak.
Direban ya yi nasarar tserewa daga kwanton ɓaunar, kuma dukkan mutanen da ke cikin motar sun tsira ba tare da wata matsala ba.
Yankin Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe ya shaida hare-haren ‘yan bindiga a watannin baya wanda ya ƙara fargabar tsaro a kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau babban birnin Jihar ta Zamfara.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, suna masu lura da cewa ana ci gaba da bincike.
Ƙoƙarin jin ta bakin shugaban ma’aikatan da wakilinmu ya yi kan lamarin ya ci tura, yayin tattara wannan rahoton.
