Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar shirya gasar Miss Nigeria ta ba fitacciyar jarumar Nollywood, Omotola Jalade-Ekeinde, haƙuri biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu, inda aka ga wata matashiyar mai gabatarwa tana tambayar ta da rashin ƙwarewa a lokacin jan carpet na taron Miss Nigeria karo na 46.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa mai gabatarwar ba ta da izinin halartar taron a matsayin wakiliyar kafafen yaɗa labarai, kuma ba ta cikin waɗanda aka tantance domin aikin.
ƙungiyar ta jaddada cewa tana matukar daraja Omotola a matsayin mamba mai muhimmanci da kuma abokiyar hulda ta kusa, wacce ta dade tana bada gudunmawa wajen bunkasa harkar fina-finai da kirkire-kirkire a Nijeriya .
Ta kuma bayyana cewa bidiyon da ya yadu bai nuna cikakken abin da ya faru ba, inda ta ce an samu lokutan da aka shiga hurumin wasu baki ba tare da izini ba, lamarin da ya sa jarumar ta ji rashin jin dadi da rashin tsaro.
A cikin bidiyon, an ga Omotola ta ki amsa tambayar mai gabatarwar da farko, tana mai cewa ba ta shirya ba, kafin daga bisani ta amince ta yi magana da ita.
ƙungiyar ta yi kira ga jama’a da ‘yan jarida da su rika mutunta dokokin taro da kuma kare martabar baki, tare da kauce wa shiga huruminsu ba tare da izini ba.
A ƙarshe, ta bukaci jama’a su goyi bayan sabon fim din Omotola mai suna Mother’s Love, wanda ke tallafawa ƙungiyar Slum2School Africa, tare da jaddada nasarar taron na shekarar 2026.
