
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinsu na faɗaɗa matakan haɗa kai da wasu ɓangarori don bunƙasa harkokin masana’antar finafinai ta Kannywood, Shugaban ƙungiyar ƴan fim ta ƙasa (MOPPAN), Mal. Mai-Kuɗi Umar da mataimakinsa na Arewa maso Yamma, Alhaji Bala Kufena, sun gana da Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB), Dakta Shaibu Hussaini a ofishinsa dake Abuja.
Jagororin na MOPPAN sun miƙa takardar neman agajin kayayyakin aiki da taron ƙara wa juna sani na haɗaka da wasu nau’ukan tattauna muhimman batutuwa da za su amfanar da Kannywood.
Wannan wani mataki ne da MOPPAN ta ɗauka don inganta harkokin masana’antar ta yadda za su dace da tsarin zamani.
Haka kuma shugabancin na MOPPAN ya fara bayyana ƙoƙarinsa na haɓaka masana’antar da nuna ƙwarewa a harkar, kamar yadda ƙungiyar ta fitar a wata takarda.
