Ta kafa sababbin kwamitoci da yin sauye-sauyen wasu
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Wakilai ta Nijeriya a ranar Alhamis ta karrama tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed.
Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa, daga yanzu, majalisar za ta riƙa biki duk ranar 13 ga Fabrairu a matsayin Ranar Murtala Muhammed, don tunawa da marigayi tsohon shugaban ƙasar.
A yayin zaman na jiya Alhamis, Majalisar wakilai ta yi shiru na minti guda, domin girmama shi, kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito.
Marigayi Murtala Muhammed ya shugabanci Nijeriya daga 1975 zuwa 1976, kafin a kashe shi a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.
An kashe Murtala ne a wani yunƙurin juyin mulki da Laftanar Kanar Buka Suka Dimka ya jagoranta, wanda bai samu nasara ba.
Bayan mutuwarsa, Janar Olusegun Obasanjo ya gaje shi, inda ya ci gaba da aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsarensa. Murtala Muhammed na ɗaya daga cikin shahararrun shugabanni a tarihin Nijeriya, kuma ana girmama shi da abubuwa da dama ciki har da filin jirgin sama na Legas da aka raɗa wa sunansa.
A wani cigaba, Majalisar Wakilai ta ƙirƙiri sabbin kwamitoci guda biyu a zamanta na jiya bayan karrama tsohon shugaban ƙasar.
An ƙirƙiro da Kwamitin kula da hukumar raya yankin Kudu maso Yamma, inda majalisar ta naɗa Hon. Akin Adeyemi a matsayin shugaba, tare da mataimakinsa Hon. Clement Akani. Sai kwamitin kula da hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya, inda shi kuma majalisar ta naɗa Hon. Tunji Olawuyi a matsayin shugaba, tare da mataimakinsa Hon. Donald Ojogo.
Waɗannan kwamitoci biyu sun ƙara yawan kwamitocin majalisar, domin tabbatar da ci gaba a yankuna daban-daban na ƙasar nan.