Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai Shari’a Folashade Ogunbanjo ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sallami tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yaɗa Labarai ta ƙasa (NBC), Ishaƙ Kawu Modibbo da Pinnacle Communications Limited tare da wanke su.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ce ta gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhumar da ake yi musu da suka shafi naira biliyan 2.5 da aka sako wa kamfanin sadarwa na Pinnacle a ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na Digital Switch Oɓer (DSO).
Da take yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai shari’a Ogunbanjo ta ce ICPC ba ta tabbatar da zargin da ake yi wa waɗanda ake tuhumar ba.
Alƙaliyar a kuma sallami waɗanda ake ƙara bisa hujjar cewa bayanai da shaidun, ba za su iya ɗora duk wani zargi kan waɗanda ake tuhumar ba.
Ta kuma ƙara da cewa wasu shaidun sun saɓa wa kansu, kuma babu ɗaya daga cikin bayanan da suka iya danganta waɗanda ake tuhumar.
A cewar alƙalin, yayin da wasu shaidun da ke cikin shaidar baka, suka ce tsohon ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed, an yaudare shi wajen amincewa da biyan Naira biliyan 2.5 ga kamfanin Pinnacle Communications Ltd, sun kasa bayar da wata shaida ƙwaƙƙwara.
An shafe shekaru shida ana shari’ar tsohon Darakta-Janar na NBC.
Hukumar ICPC ce ta gurfanar da shi da Pinnacle Communications, bisa tuhume-tuhume biyar da aka yi wa kwaskwarima kan sakin biliyan N2.5 ga Pinnacle Communications Ltd, bisa amincewar Mohammed, a ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na Digital Switch Oɓer (DSO).
