Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi.
Yusuf, wanda ya yi suna wajen sukar gwamnati, Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa.
Sai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya ce, an shirya masa tuggu ne, saboda dalilan siyasa.
Yayin da yake magana a tsare a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Yusuf ya ce, “Wannan wani yunƙuri ne na hana ni yin magana kawai. Zarge-zargen EFCC ba su da tushe balle makama, kuma suna amfani da tsofaffin maganganu marasa tushe. Ina da ƙwarin gwiwa cewa, lauyoyina za su kare ni.”
Farfesa Yusuf ya kuma zargi jami’an tsaro da bibiyar sa da iyalansa.
“Tun tsawon watanni suke bin diddigin rayuwata, a zahiri da kafafen sada zumunta. Wannan gwamnati na amfani da hanyoyin danniya, domin hana jama’a faɗin albarkacin bakinsu, kamar yadda aka saba a zamanin mulkin soja,” inji shi.
Kama shi ya jawo cece-kuce daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da kuma ’yan adawa, waɗanda suka bayyana hakan a matsayin yunƙurin muƙushe ’yancin faɗin albarkacin baki.
Wasu masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam, sun buƙaci a saki Yusuf nan take, inda suka ce suka da adawa ga manufofin gwamnati bai kamata a ɗauke su a matsayin laifi ba.
“Dimokuraɗiyya na buƙatar ra’ayoyi mabambanta. Amfani da tsoratarwa da shari’a don hana masu suka magana babbar barazana ce ga ’yancin jama’a,” inji wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam.
Duk da kasancewarsa a tsare, Yusuf ya yi alƙawarin ci gaba da magana kan yadda gwamnatin Tinubu ta gaza.
Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su zama masu lura da kuma neman haƙƙinsu a wajen gwamnati.
“Wannan ba batuna ne ni kaɗai ba. Batun kare ’yancin jama’a ne da hana kowace gwamnati amfani da tsoro don muƙushe al’umma.
“Dole mu tashi tsaye don kare haƙƙoƙinmu,” inji shi.
Yanzu haka dai yana tsare yayin da kotu ta ɗage zaman sauraron buƙatar bayar da belinsa zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.
