MOPPAN ta yi jimamin kisan gillar uwa da ‘ya’yanta shida a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar masu Shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN), ta bayyana kaɗuwarta ga Gwamnatin Jihar Kano da ɗaukacin al’ummarta bisa kisan gillar da wasu ɓata-gari suka yi wa wata uwa da ‘ya’yanta shida a Unguwar Ɗorayi Charanchi da ke jihar.

MOPPAN musamman ta kuma jajenta wa magidanta, wato Malam Haruna akan al’amarin, wanda ya girgiza al’ummar jihar da ma arewacin Nijeriya baki ɗaya.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugaban ƙungiyar, Shehu Hassan Kano, MOPPAN ta bayyana al’amarin a matsayin abin da aka yi na rashin imani da tausayi da kuma jefa ƙunci acikin jama’a.

Ta ce, wannan rashi na uwa da yaran da ba su ji ba ba su gani ba ciwo ne mai tsanani ga ba iya iyalan ba kaɗai, har ma ga al’ummar arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa, MOPPAN tana tare da gwamnatin jihar da jama’arta a yayin jimamin wannan babban rashi.

Kazalika, ta kuma jinjina wa jami’an tsaro bisa hoɓɓasa da suka yi wajen kama waɗanda ake zargi da hannu a aikata laifin tare da kira da a gaggauta zartar musu da hukuncin doka.

A ƙarshe, ta miƙa ta’aziyyarta ga Malam Haruna da makusantansa tare da fatan Allah ya ba su haƙurin juriya akan babban rashin da ya same su da kuma fatan Allah ya sanya mamatan a Aljanna.

By Babaji