
Shugaba Bola Tinubu ya karrama wani tsohon abokin hulɗarsa na harkar kasuwanci, Gilbert Chagoury, da lambar girmamawa ta Grand Commander of the Order of the Niger, wato GCON, wadda ita ce ta biyu mafi girma a Nijeriya.
Tinubu ya ce, an bai wa Chagoury lambar ne bisa guddumuwar da ya bada wajen ci-gaban Nijeriya.
A takardar bai wa Chagoury lambar yabon da ke yawo a shafukan sada zumunta, ta bayyana cewa an yi karramawar ne domin yaba wa kyawawan halayensa da ayyukansa a ƙasar.
Chagoury, wanda ɗan asalin ƙasar Lebanon ne amma haifaffen Jihar Legas, shi ne ya kafa rukunin kamfanonin Chagoury Group tare da ɗan uwansa Ronald a 1971, kamfani da ke da hannun jari a fannoni da dama ciki har da gine-gine, gidaje, masana’antu, sadarwa da fasaha.
Idan za a tuna, a shekarar 2024 ne aka yi ta ce-ce-ku-ce bayan gwamnatin Tinubu ta ba kamfanin Hitech mallakin Chagoury aikin titin Legas zuwa Calabar kan kuɗi dala biliyan 11, a sakamakon rashin bai wa jama’a dama ta neman kwangilar.
Kazalika, rahotanni sun bayyana cewa ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, na da alaƙar kasuwanci da iyalan Chagoury, a cewar PUNCH online.
