Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙara ƙarfafa tsaron jihar da isowar sabbin motocin yaƙi masu Sulke guda 8 domin yaƙi da matsalar da kuma inganta zirga-zirga a yankunan da suka fi fuskantar barazana a faɗin jihar.
Muƙaddashin gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe, ya faɗi haka bayan kammala taron majalisar tsaro na jihar.
Ya sake nanata ƙudurin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro ga dukkan al’ummar jihar biyo bayan wani lamari da ya faru kwanan nan a Gidan Mantau, cikin ƙaramar hukumar Malumfashi.
Malam Farouk Lawal joɓe wanda harwala yau shine mataimakin gwamnan jihar ya bayyana harin a matsayin “abin baƙin ciki da takaici,” amma ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri don kare rayuka.
Ya nuna manyan saka hannun jari da gwamnati ta yi a fannin tsaro, horar da ma’aikata, da kuma shirye-shiryen al’umma, ciki har da shirin ‘Community Watch’ da na ‘Yan Sa-Kai, waɗanda suka yi nasarar tabbatar da tsaro a cikin huɗu daga cikin ƙananan hukumomi takwas da su kai ta fama da hare haren ƴan bindiga a jihar da suka haɗa da Jibiya, Batsari, Safana da Ɗanmusa.
Joɓe ya sanar da cewa wannan yaƙi da ake yi da ‘yan ta’adda bai ƙare ba har sai an yi nasara.
“Ba za mu bari munanan ayyukan waɗannan ‘yan ta’adda su shagaltar da mu ba, muna yaba wa jajircewar al’ummomin yankin, waɗanda suka yi turjiya tare da fatattakar ‘yan ta’addan.
Mataimakin Gwamnan ya samar da cewa an ceto mutane 76 da aka sace , banda wasu da suka tsere a lokacin da ake ƙoƙarin sace su a garin Gidan Mantau na ƙaramar hukumar Malumfashi.
Gwamna Lawal Joɓe ya sanar da cewa ‘yan majalisar dokoki na ƙasa da ke wakilan jihar sun gana da babban hafsan tsaro da babban hafsan sojojin ƙasa domin neman ƙarin sojoji da kayan aiki a yankin Malumfashi.
Ya ce yawancin ‘yan bindigan sun koma daji, saboda yanayin ƙasa mai wahala duba da lokaci ne na Damina.
“Muna buƙatar goyon bayan Sojojin sama da na ƙasa tare da ingantaccen bayanan sirri daga al’ummar yankin.
Muƙaddashin gwamnan ya buƙaci ‘yan ƙasa da su ci gaba da amincewa da ƙoƙarin gwamnatin jihar, yana mai cewa: “Ba za a shagaltar da ku ba har sai ƙudurinmu ya tabbata, ba zamu gajiya ba har sai an tabbatar da samun ingantaccen tsaro a Jihar Katsina”inji malam Farouk Joɓe.
A nasa jawabin yayin da yake hira da manema labarai Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa, ya jajanta a madadin gwamnatin Jihar Katsina ga waɗanda hare haren ƴan bindiga ya shafa da kuma yaba wa ƙoƙarin da haɗin gwiwa na jami’an tsaro kan yadda suke yaƙar ta’addanci a jihar.
“Muna jajantawa ‘yan uwanmu maza da mata na Unguwar Mantau, Karfi, Malumfashi,”inji kwamishinan.
Ya sanar da cewa mutane mutane 28 suka rasa rayukansu a halin da ya bindigan suka ƙone masallaci na Gidan Mantau tare da ceto mutane 72 daga hannun ƴan bindigan.
Ya bayyana ta’addan ci akan wani abu ne mai haɗari wanda ke buƙatar dabarun yaƙi da na sulhu.
Dr Ɗanmusa bayyana cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa ya kashe sama da ₦36 biliyan a fannin tsaro. In banda Jihar Borno, Jihar Katsina ke kan gaba wajen samar da manyan kayan aikin tsaro a yankin,” Muna da manyan motoci na yaƙi masu sulke guda 43, ciki har da sabbin motoci guda 8 da aka kawo a baya baya nan,”Dr Ɗanmusa ya bayyana haka.
Kwamishinan yayi kira ga al’ummar jihar da su rinƙa bada bayanai na sirri da zai taimaka wa jami’an tsaro wajen zaƙulo maɓoyan ƴan ta’adda a faɗin jihar.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar ƙudirin gwamnatin jihar na ci gaba da nuna gaskiya a cikin dukkan saka hannun jarinmu a fannin tsaro,” Dr Ɗanmusa ya ce.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Kwamishinan yaɗa labarai, Dr. Salisu Zango, Darakta-Janar na Ma’aikatar yaɗa labarai, Maiwada Dan Mallam, da sauran manyan jami’an gwamnati.
