Mu ƙara ƙoƙari wajen gyaran maƙabartu don kyautata goben mu – Sarkin Amowu Odofin

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

An shawarci al’ummar Musulmin Arewa mazauna jihohin Kudu da yammacin Nijeriya da su ƙara ƙoƙari a wajen gyaran maƙabartunsu, gidajensu  na gaskiya a ranar gobe kiyama.

Mai martaba Sarkin al’ummar Hausawan ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin garin Legas Alhaji Adamu Aliyu ɗan asalin jihar Jigawa da mai martaba Sarkin Hausawan Festac Alhaji Mustapha Musa ɗan asalin jihar Katsina sune suka nemi hakan a lokacin da sarakunan guda biyu suka jagoranci waɗansu daga cikin sarakunan ƙabilun Musulman arewacin Nijeriya da matasa mazauna jihar Legas a wajen aikin gaiyya na noman maƙabarta tare da gyaranta gaba ɗaya.

Noman makabatar wanda ya gudana a makabatar unguwar Alaba Okokomaiko dake kan titin Badagiri a cikin garin Legas.

Sarakunan ƙabilun waɗanda suka haɗa da mai martaba Sarkin Hausawan Festac Alhaji Mustapha Musa da mai martaba Sarkin Hausawan ƙaramar Hukumar Amuwo odofin Alhaji Adamu Aliyu da mai martaba Sarkin Barebarin Unguwar Alaba Okokomaiko da sauran waɗansu sarakunan ƙabilun Arewacin Nijeriya da sauran matasa mazauna unguwarni daban-daban na yankin Legas ta yamma gaba ɗaya.

Da yake cigaba da tsokaci a wajen aikin gayyar noman makabartar ta unguwar Yzanasace Sarkin Hausawan na Festac Alhaji Mustapha Musa Festac bayan ya kammala nuna farin ciki tare da jin daɗinsa na samun halartar aikin gayyar makabartar ya cigaba yin kira da yabawa matasan yankin bisa ga haɗin kan da suke badawa idan irin wannan aikin na maƙabartar ya taso.

Shi ma a nasa tsokacin a wajen aikin gyaran maƙabartar mai Martaba Sarkin Hausawan Karamar Hukumar Amuwo Odofin Alhaji Adamu Aliyu ya cigaba da shawartar sarakunan Hausawan yankin da su cigaba da haɗa kawunan junan su a wajen gudanar da irin wannan aikin lada, ya ce domin kuwa wannan makabarta ta kowa da kowace babu bambancin yare kona ƙabila idan dai mutum Musulmi ne Allah ya ya yi masa wa’adi a kawo shi wannan makabarta a yi masa sutura, inji shi. 

Ya kuma yi fatan Allah Ubangiji ya jiƙan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya kyautata tamu bayan tasu.

Sauran jawaban da suka fito daga bakunan sauran sarakunan waɗanda suka samu yin tsokaci a wajen aikin gyaran maƙabartar dukkan jawabansu sun karkata ne a wajen kiraye-kiraye ga sauran sarakunan al’umma mazauna jihar Legas da su cigaba da bada himma a wajen gudanar da irin wannan ayyuka masu muhimmaci. 

By ukarofi