Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa tana ci gaba da jajircewa wajen bunƙasa shigar jama’a cikin harkokin kuɗi, don ƙarfafa tattalin arziki, musamman ga matasa da mata, yayin.
Yayin da ya ƙaddamar da sabon reshen Signature Bank a Kano ranar Talata, gwamnan ya ce, zuwan Signature Bank Kano hujja ce ta yadda jihar ke ƙara zama cibiyar kasuwanci mai jan hankalin masu zuba jari. Ya sha alwashin bai wa bankin cikakken haɗin kai tare da tabbatar da sauƙaƙa yanayin kasuwanci a jihar.
Yusuf ya bayyana cewa, tsarin tattalin arzikin gwamnatinsa na da tushe a kan aarfafa ƙanana da Matsakaitan Harkokin Kasuwanci (SME), kasancewar su ne ginshiƙin ƙirƙirar ayyukan yi, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa arziki.
“Gwamnatin mu na buɗe ƙofofi ga duk wasu bankuna da cibiyoyin kuɗi domin haɗin gwiwa wajen samar da yanayi mai sauƙi da tasiri ga masu kasuwanci.”
Ya yaba da rawar da bankuna ke takawa ta fuskar ayyukan jinƙai, musamman wajen tallafawa matasa, ƙara damar samun aiki da inganta ci gaban tattalin arziki. Haka kuma ya gode wa al’ummar Kasuwar Sabon Gari bisa bin dokokin haraji, yana kiran su da su ci gaba da taka rawar su wajen inganta kuɗaɗen shiga na jihar.
Da yake jawabi, Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya ce zurfafa harkokin kuɗi da samar da sauƙin samun kuɗi ga jama’a muhimmin ginshiki ne na ci gaban tattalin arziki. Ya tabbatar da cewa Kano na da kasuwa mai ƙarfi, kuma Signature Bank ba za ta yi nadamar shiga jihar ba.
A cikin jawabinsa, Daraktan Signature Bank, Mista Niɗon Iwedi, ya nuna godiya bisa kyakkyawar tarbar da aka yi musu, tare da tabbatar da aniyar bankin na kawo sabbin tsare-tsare na zamani da za su taimaka wa harkokin kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki a Kano.
Bikin ya sami halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin kasuwanci da sauran manyan baƙi — shaida ce ta yadda ake ƙara samun tabbataccen amincewa da yanayin kasuwanci a Kano a ƙarƙashin mulkin Gwamna Yusuf.
