NNPC na ƙoƙarin ninka hannun jarinsa zuwa kashi 20 a matatar Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta hannun Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC) ta sanar da shirin ƙara hannun jarinta a matatar mam fetur ta Dangote daga kashi 7.2% zuwa kashi 20%, a wani mataki da ake ganin zai ƙarfafa ikon Nijeriya wajen tace mai a gida da rage dogaro da shigo da man waje.

Hakan ya fito ne daga bakin Babban Daraktan NNPC, Bayo Ojulari, yayin wani taron masana’antar mai da aka gudanar a birnin Abu Dhabi (ADIPEC 2025).

Ya ce wannan shawara na nuna burin gwamnati na ƙarfafa Nujeriya a masana’antar makamashi da kuma tabbatar da tsaron makamashi na ƙasa.

Ojulari ya bayyana cewa ƙara jarin zai bai wa NNPC damar shiga zurfi a harkar sarrafa mai a gida, musamman a daidai lokacin da kamfanin ke ci gaba da neman abokan fasaha da masu zuba jari don farfaɗo da tsoffin matatun man ƙasar nan — na Kaduna, Fatakwal da Warri — waɗanda suka daɗe ba sa aiki duk da biliyoyin da ake kashewa a kansu.

A makonnin baya, Aliko Dangote ya shaida cewa ya na shirin fitowa da kashi 5–10% na hannun jarin kamfanin matatar zuwa kasuwar hada-hadar hannayen jari a Nijeriya (NGɗ) cikin shekara guda. Dangote ya ce burin sa shi ne a buɗe damar saka jari ga al’umma, amma zai ci gaba da riƙe rinjaye da kashi 65–70%.

Idan matatar Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana ta kai cikakken aiki tare da farfaɗo da matatun gwamnati, masana sun ce Nijeriya na da yuwuwar cimma ‘yancin kai a fannin samar da man fetur — abin da ƙasar ta shafe kusan shekaru 30 tana nema.

A cewar Ojulari, NNPC na kuma ci gaba da tafiyar da shirinta na fitowa kasuwa (IPO), kamar yadda doka ta PIA ta tanada, tare da ci gaba da wallafa bayanan kuɗaɗen shiga da ayyukanta don nuna gaskiya da rikon amana.

“Muna gina kamfani da ‘yan Nijeriya za su yi alfahari da shi, mai cin gashin kai, mai riba, kuma mai gogayya da manyan kamfanoni a duniya,” inji shi.

By ukarofi