Mun haramta Hawan Sallah a Kano bisa shawarar gwamnatin jihar – ‘Yan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta sanar da hana gudanar da Bikin Hawan Sallah a yayin Sallah Ƙarama ta 2025 sakamakon waɗansu dalilai na tsaro, don cigaba da wanzar da zama lafiyar al’umma.

Kwamishinan rundunar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Bompai a jihar, ranar Juma’a.

Bakori ya ce, lallai akwai buƙatar su kula da zaman lafiyar al’umma a yayin gudanar da bukukuwa.

Ya bayyana cewa, akwai barazanar tsaro a jihar wanda hakan ka iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma, lamarin da bayanan sirri suka nuna.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa, hukumar ta baza jami’ai a wurare mabanbanta da za su yi aiki a yayin gudanar da Sallar Idi domin tabbatar da tsaro a gare su.

Kazalika, ya yi kira ga jama’a da su bai wa jami’an haɗin-kai wajen tabbatar tsaro da kuma ƙaurace wa amfani abubuwan da za su haifar da zargi.

Har’ilayau, rundunar ta haramta yin Kilisa, wato guje-guje da dawakai da tseren mota gami da tuki na ganganci.

By Babaji