
Daga BELLO A. BABAJI
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addini, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi a Nijeriya da su fara duba watan Ƙaramar Sallah, wato Shawwal daga ranar Asabar, 29 ga watan Maris.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin mashawarta na harkokin addini a majalisar Sarkin, ya ce ganin watan zai bada damar sauke azumi da kuma gudanar da shungulan Sallar ta Eid el-fitr.
Ya kuma yi kira ga al’umma su ruwaito duk wani sahihin labari na ganin watan ta lambobi kamar haka: 08037157100, 08066303077, 08035965322, 08035945903, 07067146900.
Kazalika, ya kwaɗaitar da kowane musulmi da ya shiga sahun masu ƙoƙarin duba watan ganin yadda ya ke da muhimmanci wajen sanar da kammala azumin watan Ramadan da kuma gudanar da bikin sallah.
