Sojoji sun kashe jagoran ƴan bindiga, Ɗan Isihu a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, dakarun tsaro na Operation ‘FANSAN YAMMA’, sun yi nasarar kashe shahararren jagoran ƴan bindiga, Ɗan Isihu a wani atisayen sirri da sojoji suka gudanar.

A ƴan shekarun nan ne ɗan bindigar ya adabi yankuna da dama a Jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna, inda ya shahara da garkuwa da mutane da kai hare-hare gami da tarwatsa garuruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan al’umma da ɗaiɗaita wasu da dama.

Haka kuma, Ɗan ta’addar ya kasance mai tilasta wa ƙauyuka biyan haraji, gudanar da muggan makamai, ƙwace dabbobi da sauransu a yankin, lamarin da ya haifar da zaman ɗar-ɗar acikin al’ummar yankunan.

An kuma zargi ɗan ta’addar da hannu a garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa na hanyar Abuja-Kaduna, wanda a sanadiyyar haka ya samu maƙudan kuɗaɗen fansa da suka taimaka wa ƙarfafa dabarsa wajen cigaba da tada zaune-tsaye a shiyyar.

Bugu da ƙari, ayyukansa sun cigaba da firgita al’umma sakamakon hare-hare da ya ke kai wa masallatai da ƙauyuka a cikin watan Ramadana da musulmai ke gudanar da azumi.

Kisan ƙasurgumin ɗan ta’addar wata nasara ce gagaruma da za ta taimaka wajen farfaɗo da zaman lafiya da cire zaman firgici da ya jefa al’umma aciki.

By Babaji