Mun kashe Naira biliyan 2.4 don ɗaukar nauyin ɗalibai 41 a ƙasar Masar – Gwamnatin Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa ta kashe naira biliyan 2 da miliyan ɗari 200 domin ɗaukar nauyin ɗalibai 41 da ke karatun aikin likita a ƙasar Masar.

Shirin yunƙuri ne da gwamnatin jihar ta yi don magance matsalar ƙarancin likitoci a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe, ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, inda ya ce kuɗaɗen sun haɗa da kuɗaɗen karatu, wurin kwana, sufuri, da sauran kuɗaɗen da ɗaliban za su kashe a yayin gudanar da karatun na su.

Joɓe, ya bayyana irin ƙalubalen da jihar ke fuskanta wajen samun isassun likitoci da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa a baya-bayan nan an ɗauki sama da ma’aikatan lafiya 250 a matsayin wani ɓangare na matakan shawo kan ƙarancin ma’aikatan lafiya a jihar.

A cewar shi, gwamnatin jihar ta faɗaɗa tare da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 146 a faɗin ƙananan hukumomin jihar 34, inda ta mayar da su cibiyoyi masu gudanar da cikakken aikin kula da lafiya.

Kazalika, gwamnatin ta ƙara inganta cibiyoyin kiwon lafiya huɗu a ƙananan hukumomin Rimi, Faskari, Ɗanmusa, da Zango kan kuɗi Naira miliyan 3.7.

Mataimakin gwamnan ya kuma ce an inganta asibitin Janar Amadi Rimi, da ke babban birnin jihar tare da samar da injinan wankin ƙoda na zamani kan kuɗi Naira miliyan 681, inda aka sanya shi ɗaya daga cikin mafi inganci a ƙasar nan.

Ta ɓangaren samar da magunguna gwamnatin ta bayyana cewa an samar da muhimman magunguna, inda aka sayo magungunan da suka kai sama da Naira biliyan 3 daga manyan kamfanonin harhaɗa magunguna kuma an rarraba su ga cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu ana kan gina wani kamfanin harhaɗa magunguna na zamani akan kuɗi naira biliyan 1.6.

Daga ƙarshe Joɓe, ya kuma tabbatar wa mazauna jihar ƙudurin gwamnati na inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

By ukarofi