Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya buƙaci Shugaban ƙasa Ahmad Bola Tinubu da ya ƙara taimaka ma Jihar Kano da hanyoyi da za su kawo ma jihar cigaba.
Gwamnan ya bayyana hakane yayin da ya bi ayarin sauran wasu gwamnonin ƙasar nan taya shugaban ƙasar murnar shigowa sabuwar shekarar nan ta 2025 a Jihar Legas.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran shi Sanusi Ahmad Bature ya fitar ga manema labarai.
Haka kuma Gwamna Abba kabir yace kawo ayyukan cigaban da gwamnatin tarayya za tayi zai taimaka wajen zuwan masu zuba jari, bama gudanar da kasuwanci ba kaɗai har da wasu abubawan da za su bunƙasa tattalin arziki.
Sanarwar tace gwamnan ya bi sahun takwarorin shi gwamnoni ƙarƙashin jagorancin ciyaman na gwamnonin Nijeriya watau Gwamnan Jihar Kwara Dakta Abdulrazak Abdulrahman da suke fatan wannan sabuwar shekarar ta zama shekarar samun cigaba a ƙasar nan.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin shi na aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen samo hanyoyin da za su kawo ma jihar cigaba wajen samar da ayyukan raya ƙasa musamman fannin kiwon lafiya, ayyukan raya ƙasa, ilimi da hanyoyin da zasu kawo bunƙasar tattalin arziki.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya kuma yi fatan ayyukan cigaba a wannan sabuwar shekara ga Jihar Kano da ɗaukacin ƙasar Najeriya baki ɗaya
