Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi ya rasu a haɗarin mota

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Allah ya yiwa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi, Hon. Bala Arzika Kanwa rasuwa, ya rasa ranshi a sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi yau da safe a kan hanyar Ƙaura Namoda zuwa Zurmi.

Haɗarin ya faru ne a sakamakon taho mu gama da wata motar ɗaukar kaya wanda nan take Allah ya karɓi rayuwar Marigayi Hon. Bala Arzika Kanwa.

Da yake nuna alhinsa, gwamna Dauda Lawal a shafin sa na sada zumunta (Facebook) ya fara da cewar, Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, Na samu labari mara daɗi na rasuwar Mataimakin Ƙaramar gukumar Zurmi, Bala Arzika Kanwa sakamakon haɗarin mota da ya rutsa dashi yau da safe.

“Lallai wannan babban rashi ne ga ɗaukacin al’ummar Zurmi da ma Jihar Zamfara, Allah ya jiƙanshi da rahama, ya kyautata makwancinshi. Ameen”. A cewar gwamna Dauda Lawal.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Dauda Lawal a ranar 17 ga watan nuwamban da ta gabata na shekarar 2024 ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 14 bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi a jihar, tare da mataimakansu baki ɗaya.

Tuni aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin musulumci ya tanada.

By ukarofi