Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An yaba wa Alhaji Lawwali Dan’aggo bisa irin karamci da ya nuna na soma bai wa waɗanda tun farko suke zaune a wajen da aka gina katafaren rukunin kantuna na ɗan’aggo wani babban a ɗan kasuwa a Kano kuma tsohon kakakin majalisar kansiloli na ƙaramar hukumar Nasarawa.
Hon. Sa’idu Uba Ahmad Abiola ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce babu abinda za su ce da Alhaji Lawwali ɗan’aggo sai dai addu’ar Allah ya saka masa da alkhari, domin ya gina wajen kasuwanci na ɗan’aggo da kyakkyawan nufi na alkhairi da taimako domin a lokacin da zai gina ya hana kowa ya zauna bayan ya sayi wajen ya rushe ya gina, sannan ya ce sai ya bai wa mutane da suke a wajen tun ainihi sun fara zuwa sun zaɓi inda za su zauna kafin a bai wa kowa.
Hon. Sa’idu Uba ya ce sai da aka kira masu asalin shaguna a wajen na ainihi suka zaɓa duk da ƙannen sa da abokan arziƙi sun zo suna buƙatar wurin amma ya ce a’a, wanda ya tarar a wurin sai sun duba sun zaɓa. Haka kuma aka yi wanda yake zaune a baya a dana tsakiya duk sun dawo gaba yanzu wannan ya nuna adalci matuƙa.
Ya ƙara da cewa adalci na biyu da ya nuna ya zo ya sa wurin a sassauƙan farashi da ƙananan ‘yan kasuwa da manya za su mallaki wajen, sannan ya yi wa wajen tsari na adashin gata duk wanda yake so ya saya ko kuɗinsa bai cika ba ko haya ne ya kama ya kasa kayansa a hankali ya cika, in kuma saye ma za ka yi ka zo ka ɗauki wanda ya yi maka ka riƙa bayarwa a hankali an yi haka ne domin cigaban matasa da kasuwanci na jihar Kano a yadda Kano kasuwanci ya bunƙasa take ita ce cibiyar kasuwanci na ƙasa gaba ɗaya ya yi abinda yakamata.
Wani adalci da ya yi don ci gaban kasuwanci a jihar Kano wannan plaza ya gina shaguna manya da ƙanana kuma idan ka karɓi shago ɗaya to kana da shago uku haka in ka karɓi uku kana da shago 9 haka in ka karɓi shago huɗu da kana da 12 haka in kana da shida kana da 18 ya gida su manya da ƙanana sama da ƙasa hawa biyu ƙasa, ka yi kasuwanci sama ka ajiye kayanka sama ka yi ofis kuma duk wannan kuma cikin farashi mai sauƙi, saboda haka yake kiran ‘yan kasuwa manya da ƙanana da kamfanoni da su zo ɗan’aggo plaza za su ji daɗin kasuwanci.
Hon. Sa’idu Uba Ahmad Abiola ya yi fata da kira ga ‘yan kasuwar Jihar Kano su yi koyi da ɗan’aggo wanda ya gina wannan waje bisa adalci da sauƙaƙawa ‘yan kasuwa musamman matasa domin haɓaka cigaban kasuwanci a jihar Kano.
