Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya bayyana cewa, rikicin siyasa da ya daɗe yana ci gaba da taɓarɓarewa tsakanin tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, da tsohon mataimakinsa, Alhaji Atiku Abubakar, na iya ci gaba wanzuwa har sai bayan ransu.
Sanata Sani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ, yayin da yake tsokaci kan sabon musayar yawu tsakanin tsoffin abokan tafiyar siyasar, waɗanda dangantakarsu ta yi tsami sama da shekaru 20 da suka gabata.
A cewarsa, rikicin ya daɗe matuƙa har ya ratsa tsararraki, domin ya fara ne lokacin da yawancin matasan da ake kira Gen Z ke makarantar yara ko firamare, kuma har yanzu yana ci gaba bayan sun kammala jami’a, sun yi aure tare da haihuwa.
Ya rubuta cewa: “Rikicin Obasanjo da Atiku ya fara ne lokacin da ‘yan Gen Z ke makarantar yara da firamare. Yanzu kuwa suna gama jami’a, sun yi aure, sun haifi yara, amma rikicin bai ƙare ba.”
Ya ƙara da cewa, ba ya ganin wannan gaba za ta zo ƙarshe nan kusa.
“Sai dai wataƙila zai ci gaba har sai ɗayansu ya rasu, sannan ɗayan ya yi masa jawabin ta’aziyya mai cike da yabo. Tun bayan Atiku ya jefa wa Obasanjo abin da zan kira ‘babban bom’ na siyasa, Obasanjo ke ci gaba da mayar masa da martani mai ƙarfi tsawon shekaru ashirin,” inji Shehu Sani.
Kalaman nasa sun biyo bayan sabon sa-in-sa tsakanin Obasanjo da Atiku, wanda ya sake tayar da ɗaya daga cikin rikice-rikicen siyasar Nijeriya mafi daɗewa.
Sabuwar takaddamar ta samo asali ne bayan Obasanjo ya bayyana cewa zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999 shi ne kuskure mafi girma da ya taɓa yi a lokacin mulkinsa.
Obasanjo da Atiku sun kafa gwamnati tare bayan nasarar da suka samu a zaɓen 1999 a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, inda Obasanjo ya zama Shugaban Ƙasa, Atiku kuma Mataimakin Shugaban ƙasa.
A farkon wa’adinsu, Atiku ya kasance ɗaya daga cikin mataimakan shugaban ƙasa mafi tasiri a tarihin Nijeriya, inda ya jagoranci Majalisar Kula da Keɓance Kamfanonin Gwamnati (National Council on Privatisation) tare da taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, ciki har da sayar da wasu kamfanonin gwamnati ga masu zaman kansu da jawo masu zuba jari.
Sai dai bayan sake lashe zaɓen 2003, dangantakarsu ta fara lalacewa sakamakon sabanin ra’ayi kan magajin Obasanjo, shugabancin jam’iyya, naɗe-naɗe da kuma tasirin Atiku a siyasa.
Rikicin ya ƙara muni lokacin da magoya bayan Obasanjo suka yunƙura wajen yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin ba shi damar yin wa’adi na uku.
Atiku ya fito fili ya nuna adawarsa ga wannan yunƙuri, lamarin da aka ɗauka a matsayin ƙalubalantar shugaban ƙasa kai tsaye.
A shekarar 2006, Majalisar Dokoki ta ƙasa ta yi watsi da ƙudirin wa’adi na uku bayan gagarumar adawa daga ‘yan majalisa, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Bayan haka ne Obasanjo ya zargi Atiku da rashin biyayya, cin hanci da kuma yi wa gwamnatinsa zagon ƙasa, yayin da Atiku ke cewa ana gallaza masa ne saboda ya ƙi goyon bayan wa’adi na uku.
Rikicin ya kai kotu bayan ficewar Atiku daga PDP zuwa Action Congress (AC) kafin zaɓen 2007, inda gwamnatin Obasanjo ta yi ƙoƙarin ayyana kujerarsa a matsayin wadda ta zama fanko.
Sai dai Kotun ƙoli ta yanke hukunci a watan Maris na 2007 cewa shugaban ƙasa ba shi da ikon tube mataimakin shugaban ƙasa da aka zaɓa, wanda hakan ya bai wa Atiku damar kammala wa’adinsa.
Tun bayan barinsu mulki, Obasanjo da Atiku sun ci gaba da musayar zarge-zargen cin hanci, amfani da mulki ba daidai ba da cin amanar juna.
Ko da yake sun ɗan sasanta kafin zaɓen 2019, lokacin da Obasanjo ya goyi bayan takarar Atiku, wannan sulhu bai daɗe ba, domin daga baya suka koma ci gaba da suka da juna.
Sabuwar takaddamar ta sake ƙamari ne bayan Obasanjo ya zargi Atiku da bai wa marigayi Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba, cin hanci domin tsige shi daga mulki.
Atiku ya musanta zargin tare da cewa tsohon shugaban ƙasar na ƙoƙarin bata masa suna kafin zaɓen 2027.
Daga nan ne Obasanjo ya sake jaddada cewa zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa shi ne kuskure mafi girma da ya yi, yayin da sansanin Atiku ya yi watsi da wannan iƙirari, lamarin da ya sake buɗe tsoffin raunukan siyasa tsakanin jagororin biyu.
