Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ce malamai da ke shiga siyasa domin kawo gyara sun fi waɗanda ke takaita kansu ga yi wa ‘yan siyasa addu’a ba tare da shiga cikin tsarin mulki ba.
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan rawar da ya kamata malaman addini su taka a siyasa, musamman bayan yadda wasu fitattun malaman Musulunci suka shiga harkokin gwamnati da siyasa.
A cewarsa, idan malami yana da niyyar tabbatar da adalci da kyakkyawan shugabanci, shiga siyasa ba laifi ba ne. Ya ce tarihin Musulunci ya nuna cewa malamai sun kasance masu ba da gudunmawa wajen tafiyar da mulki, don haka bai kamata a raba addini da shugabanci gaba ɗaya ba.
Kalaman na Gumi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan matakin tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda ya shiga siyasa tun lokacin da aka naɗa shi minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sannan daga baya ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC. Matakin Pantami ya jawo martani mabambanta daga malamai, ‘yan siyasa da mabiyansa, inda wasu ke ganin ya dace malami ya shiga siyasa domin kawo sauyi, yayin da wasu ke ganin ya kamata ya tsaya kan wa’azi da karantarwa.
A watannin baya, Pantami ya shiga takaddama da shugabannin APC a Gombe bayan ya ƙi amincewa da tsarin fitar da ɗan takarar gwamna ta hanyar maslaha (consensus), yana mai cewa ya fi dacewa a bar wakilai su zaɓi wanda suke so.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin kalaman Sheikh Gumi za su ƙara ƙarfafa muhawarar da ake yi kan matsayin malaman addini a siyasar Nijeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, inda fitattun malamai irin su Pantami ke neman manyan muƙaman siyasa
