Nijeriya ta tura sojoji 86 aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta tura jami’ai 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce matakin ya nuna ci gaba da jajircewar Nijeriya wajen tallafa wa zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka ta Yamma, inji sanarwar.

Sanarwar ta ce jami’an sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya domin fara aikinsu ƙarƙashin umarnin ECOWAS, inji sanarwar.

Rundunar ta bayyana cewa Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen Afirka da suka fi ba da gudunmawa wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya na ECOWAS, Tarayyar Afirka da kuma Majalisar ɗinkin Duniya, inji sanarwar.

Ta ƙara da cewa sabon aikin ya sake nuna muhimmiyar rawar da Nijeriya ke takawa wajen hana rikice-rikice, gina zaman lafiya da dawo da kwanciyar hankali a ƙasashen Afirka, inji sanarwar.

An kafa rundunar wanzar da zaman lafiyar ne domin tallafa wa ɓangaren tsaro da inganta yanayin siyasa a Guinea-Bissau, bayan shekaru ana fama da rikice-rikicen siyasa da juyin mulkin soja.

Nijeriya ta daɗe tana cikin ƙasashen da suka fi tura dakaru zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya na ECOWAS, inda ta ba da gudunmawar sojoji, kayan aiki da jagoranci a ƙasashe irin su Laberiya, Saliyo, Gambiya da Guinea-Bissau.

By ukarofi

Leave a Reply