Maigwari II ya yaba wa Tinubu, ya nemi a faɗaɗa aikin sake gina hanyar Kaduna-Birnin Gwari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Maigwari II, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa cika alƙawarin da ya ɗauka na sake gina hanyar tarayya ta Kaduna (Mando) zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 122, tare da roƙon Gwamnatin Tarayya ta faɗaɗa aikin zuwa sauran sassan hanyar da suka fi lalacewa.

Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ƙaddamar da aikin sake gina hanyar, inda ya bayyana aikin a matsayin wani gagarumin ci gaba ga al’ummar masarautarsa.

Ya ce fara aikin ya cika burin da al’ummar yankin suka daɗe suna fata, tare da buɗe sabon babi na farfaɗo da tattalin arziki, inganta tsaro da samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya tuna cewa lokacin da Tinubu ya kai ziyara Birnin Gwari a ranar 2 ga Disamba, 2022, ya duba mummunan halin da hanyar ke ciki tare da yin alkawarin inganta tsaro da sake gina hanyar.

Sarkin ya ce yanzu alkawuran sun zama gaskiya, yana mai gode wa Shugaba Tinubu bisa tsayawa tare da al’ummar Birnin Gwari a lokacin da suke cikin ƙalubale, inji shi.

Ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a harkar tsaro a masarautar, lamarin da ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu, kasuwanni suka farfaɗo, yayin da mazauna yankin suka sake samun kwarin gwiwa.

Haka kuma, ya yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa ƙoƙarinsa na inganta tsaro da samar da ababen more rayuwa, wanda ya taimaka wajen fara aiwatar da aikin.

Sarkin ya kuma yabawa Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, yana mai cewa hanyar na da matuƙar muhimmanci wajen haɗa Arewa da Kudancin Nijeriya ta fuskar kasuwanci da harkokin noma.

Sai dai ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta fara aikin daga ɓangaren Birnin Gwari zuwa Udawa, wanda ya ce shi ne mafi lalacewa a duk hanyar.

Ya kuma buƙaci a ba hanyoyin Birnin Gwari–Kaduna, Birnin Gwari–Tuwa da Birnin Gwari–Funtua kulawa, saboda muhimmancinsu ga noma, kasuwanci da haɗin kan ƙasa.

Sarkin ya tabbatar wa gwamnati da cewa masarautar za ta ci gaba da wayar da kan al’umma domin kare aikin, ba da haɗin kai ga kamfanin da ke aiwatar da shi da kuma tabbatar da zaman lafiya, inji shi.

A nasa jawabin, ƙaramin Ministan Ayyuka, Bello Goronyo, ya ce aikin wata alama ce ta ƙudirin gwamnatin tarayya na bunƙasa ababen more rayuwa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda.

Ya ce hanyar mai tsawon kilomita 122 za ta ƙarfafa kasuwanci, zuba jari da zirga-zirgar kayayyaki da mutane, tare da rage kuɗin sufuri, samar da ayyukan yi da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

Goronyo ya ce aikin ya cika ɗaya daga cikin alkawuran yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu ga al’ummar Birnin Gwari, inji shi.

Shi ma Manajan Daraktan kamfanin J. Patel and Sons Ltd., Urmil Patel, ya tabbatar da cewa kamfanin ya kammala shirye-shiryen fara aikin, yana mai cewa za a kammala shi cikin watanni 24 kamar yadda kwangilar ta tanada.

Ya ce aikin ya haɗa da gyaran gadoji tara da magudanan ruwa 93, tare da samar da guraben aiki ga ɗaruruwan matasa daga al’ummomin da ke kan hanyar, inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply