Wike ya ƙaƙaba takunkumi kan ayyukan ‘yan acaɓa da masu adaidaita sahu a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce gwamnatin birnin ta kammala shirye-shiryen sake fasalin ayyukan babura da adaidaita sahu (Keke Napep) a Abuja, domin magance matsalolin tsaro da kuma inganta doka da oda.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ganawarsa ta wata-wata da manema labarai a Abuja.

Ya ce ayyukan babura da adaidaita sahu sun zama barazana ga tsaro a babban birnin tarayya, saboda haka ya zama dole a taƙaita zirga-zirgarsu zuwa wuraren da gwamnati za ta ware musu.

Ministan ya bayyana ayyukansu a matsayin abin da ke kawo cikas ga tsarin birnin, yana mai jaddada cewa ba za a bari su ci gaba da aiki a tsakiyar birnin Abuja ba, bisa tanadin dokokin da ake da su.

Ya ce ya umarci hukumomin tsaro su tantance yankunan da za a ba su damar gudanar da ayyukansu, tare da hana su shiga wasu muhimman wurare.

“Da safiyar yau na sanya hannu kan amincewar wannan mataki bayan taron Majalisar Tsaro. Mun fahimci cewa ba wai kawai suna kawo cikas ba ne, har ma sun zama barazana ga tsaro,” inji shi.

Sai dai Wike ya ce zai yi wahala a haramta ayyukan babura da adaidaita sahu gaba ɗaya a Abuja, saboda haka gwamnati za ta takaita ayyukansu ne zuwa wasu wurare da aka amince da su, inji shi.

Haka kuma, ministan ya nuna damuwa kan yadda mabarata da masu yawon banza suka mamaye titunan Abuja.

Ya ce duk lokacin da gwamnati ta kwashe su daga tituna, sukan sake dawowa, yana mai bayyana cewa gwamnatin yanzu ba za ta iya ci gaba da samar musu da matsuguni ba.

Wike ya ce gwamnati na ƙoƙarin samar da dabarun da za su magance matsalar, kuma tana jiran amincewar wasu tsare-tsaren gudanarwa da kuɗaɗen aiki.

Ya ƙara da cewa samar da matsuguni ga mabarata na iya ƙarfafa mutane daga jihohin Kogi, Nasarawa, Neja da Kaduna su riƙa kwararowa Abuja, lamarin da gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyinsa ba, inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply