Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Joɓe, ya ƙaddamar da buɗe ofishin ’yan sanda (Outpost) na wucin gadi da shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude , ya gina a Unguwar Kofar Sauri, cikin mazaɓar Wakilin Gabas I da ke ƙaramar hukumar Katsina, wanda ƙaramar hukumar Katsina ta gina domin ƙara inganta harkokin tsaro a faɗin ƙaramar hukumar.
A jawabinsa, Mataimakin Gwamnan Jihar, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad, bisa wannan aiki da ya gudanar, wanda ya ƙara tabbatar wa al’umma cewa Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ta bai wa ƙananan hukumomin Jihar Katsina baki ɗaya damar kashe kuɗaɗen su kamar yadda ya yi alƙawari, domin gudanar da ayyuka da za su amfani al’umma kai tsaye.
Haka zalika, ya yi kira ga al’ummar da su ƙara bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen gudanar da ayyukansu, domin tsaro na kowa ne, kuma kowa yana da gudummawar da zai bayar domin magance matsalolin tsaro ta hanyar bayar da bayanan da suka kamata, musamman game da mutanen ɓatagari da suke cikin al’umma.
Haka kuma, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Katsina bisa irin yadda yake gudanar da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma ta ɓangarori daban-daban.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad, ya ce: “Kamar yadda muka yi alƙawari, yau ga shi mun cika da yardar Allah, mun gina wannan waje domin ƙara inganta harkokin tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma, musamman a ƙaramar hukumar Katsina.”
Haka zalika, ya yi kira ga al’umma, musamman matasan wannan mazaɓa, da su bai wa jami’an tsaron da za su yi aiki a wannan wajen haɗin kai da goyon baya domin samar da cikakken tsaro da zaman lafiya a yankin.
A nasa jawabin, ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na Ƙofar Sauri Alh. Dikko, a madadin al’umma, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Katsina bisa irin ayyukan alkhairan da yake gudanarwa a wannan mazaɓar, da ma ƙaramar hukumar Katsina baki ɗaya, a ɓangarori daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma.
Daga cikin waɗanda suka yi magana akwai kwamishinan ’yan sanda, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, ɗan majalisar dokoki, Hon. Aliyu Abubakar Albaba, shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina, kansilan mazaɓar Gabas I, Hon. Zaharaddeen, da dai sauransu.
