Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, ya yi alƙawarin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yari ya yi wannan alƙawarin ne bayan jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) ta naɗa shi Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya gode wa Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC bisa amincewa da shi, yana mai cewa zai ɗauki nauyin da aka ba shi da matuƙar muhimmanci.
“Ina miƙa godiyata ta gaskiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar bisa amana da suka ba ni. Ban ɗauki wannan nauyi da wasa ba,” in ji Yari.
Ya ce yaƙin neman zaɓen ba wai neman ƙuri’u kawai ba ne, sai dai tattaunawa da ‘yan Nijeriya a faɗin ƙasar kan makomar ƙasar.
Yari ya yi kira ga mambobin APC da magoya bayan jam’iyyar da su fara aikin yaƙin neman zaɓen tun yanzu domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen mai zuwa.
Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya daga sauran jam’iyyu da su goyi bayan sake zaɓen Tinubu, yana mai cewa ya kamata a zaɓi ci gaba maimakon rarrabuwar kawuna.
“Da yardar Allah, da kuma ƙoƙarin dukkanmu, za mu samar da nasara a watan Janairun 2027,” in ji shi.
A baya-bayan nan ne APC ta sanar da sunayen mutum 108 da za su jagoranci yaƙin neman zaɓen Tinubu, inda aka naɗa Yari a matsayin Darakta-Janar, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, zai kasance Sakataren kwamitin.
Jam’iyyar ta kuma ayyana Shugaba Tinubu a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, za su kasance mataimakan shugaban kwamitin.
