Na zaɓi na fara rubutu ne saboda isar da saƙo – Fatima Alaramma 

Spread the love

“Na fi yin rubutu akan zamantakewar rayuwa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Akwai marubuta da dama da ke shigowa fagen harkar rubutun adabi da ƙafar dama. Yayin da wasu ke farawa da ƙalubale, amma daga baya su miƙe, wasu ƙalubalen ne ke sa su gaza cigaba da ƙoƙarin da suka fara na rubutu. Fatima Muhammad Yusuf da aka fi sani da Fatima Alaramma, na daga cikin marubutan adabi da a farko rubutu ya nemi ya ba ta wahala, amma da taimakon shugabannin ƙungiyar ta, sai ga shi yanzu tana cikin marubutan Hausa da ake damawa da su a onlayin. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa burin ta na kafa wata gidauniya da za ta riƙa tallafa wa sabbin marubuta wajen ba su horo kan dabarun inganta rubutu. A sha karatu lafiya. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

FATIMA: Da farko dai, sunana Fatima Muhammad Yusuf, wacce aka fi sani da Fatima Alaramma ko Falaramma. Ni marubuciya ce kuma makaranciyar littattafan Hausa. Sannan ina ɗan taɓa kasuwanci, da koyarwa a makarantar Islamiyya, inda harwayau kuma nake cigaba da nawa karatun, a matsayin ɗaliba. Kuma ina alfahari da hakan. Har yanzu ni budurwa ce, ban taɓa yin aure ba, amma ina gab da auren in sha Allahu. 

Zan so ki bamu tarihin rayuwarki. Karatun ki da inda ki ka yi rayuwa. Wanne matakin ki ke a yanzu.

Ni haifaffiyar garin Kano ce. An haife ni a Unguwar Sharaɗa da ke ƙaramar Hukumar Dala. Na yi karatun firamare da sakandire duka a Sharaɗa. Sannan ban tsaya a nan ba, yanzu haka ina karatun ilimin Shari’a, a Kwalejin Nazarin Ilimin Addinin Musulunci da Shari’a ta Malam Aminu Kano. Duk da ba shi ne muradina ba, amma da na karɓa kuma har ga shi cikin ikon Allah gashi yanzu ina gab da kammalawa. In sha Allahu ina watarana na zama cikakkiyar Barista, saboda hakan shi ne muradina da na mahaifina. Sai dai kuma harwayau, ina son na zama babbar ‘yar jarida, saboda hakan mafarkina ne. Shi ma in sha Allahu ina sa ran watarana zan juya na cigaba da karatun aikin jarida da yarda Allah, idan na kammala karatun na aikin shari’a da nake yi yanzu. 

Ni dai na taso da rashin son hayaniya, kuma ba ni da saurin yarda da mutane, ga rashin saurin sabo. Amma duk da hakan na kasance ina da farin jinin mutane daidai gwargwado, don tun Ina ƙarama a makaranta malamai suna nuna min ƙauna da kulawa sosai. Duk da rashin son hayaniyata za ka ga duk inda na shiga ana so na a yi hulɗa da ni, saboda bani da damuwa a rayuwata. Ina da yawan fara’a. Kuma ba a faɗa da ni sosai, saboda gaskiya ba ni da tsokana. Haka zalika ban da na son raini, shi ya sa ma ba na shiga lamuran mutane sosai.

Mene ne babban abin da yake ba ki sha’awa game da rayuwa?

Abinda yake burge ni a rayuwa shi ne, Allah Ya yi min abin da ba na tsammani, kamar baiwa, ko nasara da Allah Yake ba ni, ta cigaban rayuwa. Duk abin da na sa a raina zan yi ko wanda ban sa rai zan yi ba, sai ka ga Allah Ya yi min shi da izinin Sa, kuma babu abin da wani ya isa ya tsare min, saboda Ubangijin ne ya bani. Sannan abin da yake ƙara burgeni ga rayuwata shi ne baiwar Musulunci da Allah Ya yi min ya halicce ni a cikin al’ummar musulmai, wannan ma na ɗaya daga cikin abin da ke ƙara burgeni a rayuwa.

Wanne ƙalubalen rayuwa ki ka fuskanta a lokacin tasowarki da yadda hakan ya inganta rayuwarki?

A gaskiya ban samu wani babban ƙalubale ba a lokacin ƙuruciya ba, har sai da na fara tasowa na ƙudiri aniyar zan fara rubutu. To, a nan ne dangin mahaifina suka nuna min rashin goyon bayansu akan harkar rubutun. Haka nan dai na cigaba da addu’a kuma iyayena suka goya min baya, akan rubutun da nake yi har kawo yanzu. Kuma ko a yanzu sai dai na ce, Alhamdulillahi. Komai yana tafiya yadda ya kamata.

Kina daga cikin matasan marubuta na onlayin, ko za ki gaya mana yadda aka yi ki ka zama marubuciya?

Yadda aka yi na zama marubuciya shi ne, ni ma’abociyar son labarai ce. Kuma ni mai yawan karance-karance, duk abin da na gani a hanya sai na karanta, kuma duk abin da na ji sai na saurara, sannan kuma duk abinda na karanta sai na yi nazarinsa.

Na zaɓi na fara rubutu ne saboda isar da saƙo. Da kuma nuni ga al’umma cikin nishaɗi da hannunka mai sanda, duba da abinda ke faruwa a cikin al’ummarmu. Wannan shi ya sa na zaɓi na fara rubutu, saboda na ga mutane na bibiyar rubutun da ake yi sosai.

Na lura daga cikin dalilan da ya sa wasu ke ganin ba zan iya rubutun littafi ba, ciki har da wasu ýan’uwana, shi ne ƙanƙantar shekaruna, da kuma gidan da na taso, domin mu mun fito ne daga gidan malamai. Duba da maganar wasu mutane kan ce, wai rubutu ɓata lokaci ne, kuma abu ne marar amfani, akan haka ne ya sa na ƙarfafa gwiwata wurin tabbatar wa da mutane cewa rubutu ba aikin banza ba ne. Kuma ina ƙoƙarin nuna musu cewa, rubutu ba ɓata lokacin ba ne faɗakarwa ce, domin akwai darussa da dama a cikinsa. Alhamdulillah, tun da na fara rubutu ina cigaba da samun goyon bayan iyayena da masu bibiyar rubutuna. Gaskiya babu abin da zan ce wa Allah sai godiya.

Na fara rubutu a shekarar 2018, lokacin ina rubutu a kan littafi na takarda, har na rubuta littattafai guda uku, duka na kammala su. Sai a shekarar 2020 ne na fara rubutu a onlayin.

Waye ya fara nuna miki yadda ya kamata ki yi rubutun labari?

Wanda ya fara nuna min yadda zan yi rubutun labari a onlayin shi ne Malam Sadik Abubakar, Shugaban ƙungiyar Lafazi Writers Association. Na sha wahala sosai a lokacin da yake nuna min abubuwan. Wani lokaci idan na kwaɓa rubutun shi yake yi min gyara. Ba na mantawa watarana na taɓa ce masa, nifa na fasa rubutun nan saboda wahalar da na ke sha. Amma haka zai ce ki yi haƙuri, in sha Allahu watarana sai labari. Ya kan ce min za ki zama marubuciya yadda ba kya tunani, da izinin Allah sai kin taka wani matsayi. Haka ya kan kawo min misalin wasu mutane da suka samu nasarori a rayuwar su ta rubuta, bayan ƙalubalen da suka fuskanta a farko. Da irin wannan ƙarfafa gwiwa har na kawo haka. Alhamdulillahi, ina godiya sosai ga Malam Sadik Abubakar. 

Shin kina karanta littattafan wasu marubutan? Kuma wanne littafin ki ke karantawa a halin yanzu?

E, ina karanta littattafan wasu marubutan, amma marubuciyar da nafi karanta littafinta ita ce A’isha Aliyu Garko. A gaskiya ina son karanta littattafanta akwai faɗakarwa da nishaɗantarwa a cikinsu. Littafin da nake karantawa a halin yanzu shi ne ‘Auren Sirri’, wanda ita A’ishan ce ta rubuta shi.

Wacce marubuciya ko marubuci ne allon kwaikwayonki, ko wacce salon rubutunta ya fara sa miki sha’awar rubutu?

Marubuciyar da zan ce ita ce allon kwaikwayona kuma nake alfahari da ita a harkar rubutu ita ce, Fauziyya D. Sulaiman. Duba da yadda take gudanar da harkokinta, da yadda take taimakawa rayuwar al’umma marasa ƙarfi da tallafawa marayu da gajiyayyu da sauran jama’a.

Kawo yanzu littattafan ki nawa, kawo sunayen su?

Aƙallah yanzu na rubuta littattafai sun kai goma sha biyu. Banda gajerun labarai. Na rubuta littafin ‘Sanadinta Ne’, ‘Ciwo A Zuciya’, ‘Sanadin Ýar Alaramma’, ‘Gayya Ce’, ‘Wacece Ýar Daji’, ‘Sakaci’, ‘Butulci’, ‘Rayuwar Zainab’, ‘Sunaiha’, ‘Halina Ne’, ‘Barista Sima’, da kuma ‘Yar Talaka Ce’.

Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu akai, kuma wanne lokaci ne ki ka fi jin daɗin yin rubutu?

Ina samun jigon rubutu ne ta hanyoyi daban-daban akwai yanayin rayuwar da muke cike, da kuma abubuwan da suke faruwa ga al’ummar mu. Sau da dama kana zaune a inda ka ke ma za ka ga wani abu ya faru to, a daidai wannan gaɓar sai ka samu wani jigo. Wani lokaci kuma akan ka wani abu zai faru sai ka ga ka samu jigo a kansa. Wani lokaci kuma a yanar gizo za ka ga wata tambayar ko wani abu daga nan sai ka ga jigo ya fita. Wani lokaci kuma daga tambayoyin da ake yi wa malaman mu, a nan nake samun jigon rubutuna. Akwai wani lokaci ma kana kwance za ka ji wani abu ya faɗo maka a rai, daga nan sai ka gina jigonka. 

Sannan, na fi son na yi rubuta bayan sallar asuba ko kuma bayan sallar isha’i, lokacin da gari ya yi shiru babu hayaniya. Wannan lokacin rubutu ya fi min daɗi. Ko kuma lokacin damina, idan ana ruwan sama, gari ya yi shiru rubutu yana min daɗi. 

Wanne alheri ki ka taɓa samu a dalilin rubutu?

Na samu alkairai da dama. Akwai satifiket da na sassamu, saboda karramawa da gudunmawata. Akwai gidajen talabijin da suka gayyace ni mu yi hira. Banda ƙananan ƙungiyoyin onlayin da suke gayyata ta tattaunawa. Wani lokaci ma wani wurin ko wani taron za ka je idan ka ce kai wane ne sai ka ga ana maka alfarma kala-kala. Banda waɗanda suke saka maka data ko wasu alkairai na wani abu don ka ji daɗi. Kai, ta ko’ina ma dai mu ce Alhamdulillahi. 

Yaya ki ke sanin labarinki yana samun karɓuwa a wajen masu karatu?

Ina sani ne ta yadda zan riƙa ganin mutane na min sharhi da aiko da saƙonni, ko in ji ana cigiyar littattafan da na yi a wasu zaurukan marubuta. Wani lokaci kuma wasu masu karatun kan kira ni, domin yi min godiya, ko haɗa alaƙar zumunci da ni. Za ka ji wani lokaci wasu suna cewa suna sona, ko ina burge su. Gaskiya ta waɗannan hanyoyin nake gane labarai na sun sami karɓuwa.

Ta yaya ki ke mu’amala da masu bibiyar littattafanki?

Gaskiya ba ni da wulaƙanci duk wanda ya yi min magana nakan yi ƙoƙarin na kula shi har ma na yi hira da su, su kuma sukan faɗa min, ra’ayoyinsu a kaina. Sau da dama idan na bai wa mutane amsa ko na yi hira da su, za ka ga har da dariya ake rabuwa ana raha da juna. Sai ka ji suna cewa, gaskiya kina da kirki, bamu zaci zaki kula mu ba, saɓanin wasu marubutan da sai ka yi musu magana goma ba su baka amsar ɗaya ba.

Bayan rubutu akwai wata harka da ki ke yi ne, ta sana’a ko kasuwanci?

Ina sayar da kayan ƙamshi, turaren wuta da na jiki, da na kaya, da kuma kabbasa. Turaren wanka da na wanki da sauran su. Ina taɓa kasuwancin onlayin, ina sayar da dogayen riguna da abaya. Ina Kuma sayar da alawar madara, iloka, albishir da gullisuwa da sauran duk wani abin ci na ƙwalama. Sannan ina sayar da kanyan soye-soye irin su alkaki da cincin, dubulan, misfai da sauran su.

Bayan baiwar rubutu, wacce basira ki ke da ita wanda ba kowa ya sani ba?

A gaskiya ina da saurin iya abu, ko sau ɗaya na ga abu to, in sha Allahu in dai na saka shi a raina zan iya shi, ba ɓata lokaci da yardar Allah. Kuma duk abin da nasa a gaba da yardar Allah nakan iya shi. 

Wanne salon labari ki ka fi son rubutawa, soyayya, almara, ko zamantakewa?

Gaskiya ni ba gwana ba ce wajen soyayya, hasali ma rubutun labarin soyayya yana bani wahala sosai. Na fi yin rubutu akan zamantakewar rayuwa ta yau da kullum. Sannan kuma ni ban fiye rubutu akan kishi ba, saboda gaskiya ba ya gabana, duk da nasan wani lokaci yana da nasa illar shi ma.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako take miki a harkar rubutun adabi da ki ke yi?

Ni mamba ce a ƙungiyar Lafazi Writers Association, ina kuma alfahari da kasancewa ta a cikin ta. Gaskiya shugabannin ƙungiyar na matuƙar ƙoƙari, ba a kaina kaɗai ba, akan duk wani ɗan ƙungiyar. Suna tallafa mana, suna kuma nuna mana abubuwan da suka dace da mu yi a cikin rubutun mu. Suna ƙoƙari sosai, wajen koya wa sababbin mambobin ƙungiyar ƙa’idoji da dabarun rubutun adabi. Babu abin da zan ce wa Lafazi sai godiya. Alhamdulillahi.

Wanne ƙalubale ki ke ganin ya fi damun marubuta a wannan lokaci, wanda ya kamata su gyara?

ƙalubalen da yake damun marubuta a wannan lokaci shi ne saurin rubutu ba tare da zurfafa tunani da bincike ba. Da yawa daga cikin marubuta muna saurin rubuta labari ko ra’ayi kawai don mu cika shafuka ko mu buga littafi, amma ba lallai muna tsayawa muna tantance ingancin abin da muka rubuta ba. Wannan yana haifar da raunin harshe, raunin tsari, da kuma raunin saƙo. Har ila yau, akwai matsalar kwaikwayo da maimaita abu guda. Yawancin marubuta suna bin salon juna ko suna ɗaukar abin da suka gani ko suka karanta, a wajen wasu, a maimakon su ƙirƙiro daga hikimarsu da hangen nesansu. Wannan yana rage wa rubutu armashi da tasiri.

Sannan harwayau, akwai ƙalubalen karanta littattafai masu inganci. Idan marubuci bai zama mai karatu ba, ba zai iya gina kalmomi cikin salo da fasaha ba. Yana da kyau marubuta su ƙara mayar da hankali wajen karatu da neman ilimi don ƙara faɗaɗa basirar su. Don haka a taƙaice, abubuwan da suka kamata mu gyara sun haɗa da zurfafa tunani kafin rubutu, kaucewa kwaikwayo da maimaita abu ɗaya, mu zama masu ƙirƙira. Mu ƙara yawan karatu don inganta rubutunsu. Idan muka gyara waɗannan, za mu taimaka wa adabinmu ya bunƙasa cikin nagarta da armashi.

Idan kin samu dama wanne gyara za ki so ki kawo don cigaban rayuwar mata da marubuta ýan’uwanki?

Idan na samu dama da yardar Allah, ina son in kafa wata ƙungiya da za ta koyawa mata sana’a da kuma nuna musu mahimmancin ta gare su, musamman matan mu na karkara waɗanda mazajen su ba sa iya ɗauke musu wasu haƙƙokin su. Tabbas ina da muradin wannan. Ina so in ga na taimakawa marasa ƙarfi, ta yadda zan iya ba su jarin da za su iya yin sana’a, ko wani kasuwanci ba tare da sun biya ko sisi ba.

Sannan ina son in riƙa taimaka wa ƙananan marubuta waɗanda suke shan wahala wajen fara rubutu, saboda rashin wanda zai nuna masu wasu abubuwan. Shi ya sa nake son kafa wata babbar ƙungiyar marubuta da masu sha’awar fara rubutu. Ta yadda za su riƙa samun horo don inganta rubutunsu, da samun ƙarin ilimi a harkar rubutu da kuma ƙara gogewa wajen tafiya da zamani.

Wanne buri ki ke da shi nan gaba a rayuwarki?

Ina da burika da yawa, amma manya daga cikinsu akwai burin da nake da shi na zama shahararriyar marubucinyar da duniya za ta yi alfahari da ita. Na biyu, ina son na zama cikakkiyar lauya wacce babu irin ta a duk faɗin Kano, wacce ta samu lambar yabo wajen warware duk wata sarƙaƙiya ta shari’a, da ta sha kan sauran lauyoyi. Amma ya zama ni ce zan iya warware ta, da izinin Allah. Na uku, ina son in zama shahararriyar ‘yar jaridar da ake ji da ita a Kano, wacce za ta yi suna wajen sanin makamar aikin ta, da kuma jajircewa wajen gaskiya da riƙon amana.

Wanne karin magana ne ya fi ɗaukar hankalinki?

Sannu sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba. 

Na gode. 

Ni ce da godiya.

By ukarofi