Ƙatar ta hana maza shiga ƙasar ba tare da iyali ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Ƙatar ta samar da sabon tsarin dokokin biza sakamakon yawaitar batutuwan zama sama da ƙa’ida da karya dokokin shige da fice.

A wani saƙo da hukumar tafiye-tafiye ta TravelTank ta fitar ga kwastomominta, gwamnatin ƙasar ta ministanta na harkokin cikin gida, ta ce sababbin dokokin za su fara aiki ne a nan take.

An kafa sabon tsarin ne ta yadda zai yi aiki akan masu bizar yawon buɗe ido da na masu zama domin wasu harkoki, sannan zai shafi na waɗanda ake aiki akan sama musu biza bayan sun miƙa buƙatar hakan kafin gabatar da sabbin dokokin.

Sannan, a ƙarƙashin dokokin akwai haramta wa ƴan Nijeriya biza matuƙar za su shiga ƙasar ba tare da iyalansu ba.

Haka kuma, takunkumin yana nufin mata masu mazaje ne kaɗai suke da damar neman bizar ƙasar.

Bugu da ƙari, dokokin sun bayyana cewa wajibi ne masu neman biza su nemi masauki a otal ɗin 5-star kafin a fara aiki akan bizozinsu.

Kazalika, gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin kakkaɓe matsalolin saɓa wa dokokin shige da fice a ƙasar da tabbatar da bin ƙa’idojin tafiye-tafiye a mataki na ƙasa-da-ƙasa.

By Babaji