Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) a ranar Laraba ta ce ta gano wani ɗakin ajiye kayayyaki da aka maƙare da lita 88,560 na sinadaran hada bama-bamai a Kano.
Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a ƙofar rumbun da ke unguwar Kwakwaci a ƙaramar Hukumar Fagge da ke jihar.
Mojisola, wacce Daraktan Bincike da Tabbatar da Bin Doka na hukumar, Dokta Martins Iluyumade ya wakilta, ta ce ɗakin na ɗauke ne da lita 60,000 na sinadarin sulphuric acid, sai kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma wasu jarkoki 330 da aka riga aka rabar wa mutanen da ba a san ko su wane ne ba, sinadaran cikin su.
“Abin da muka gano yau a nan ya tayar mana da hankali matuƙa, ba na tunanin a rayuwata na taɓa ganin adadin irin waɗannan sinadaran a waje ɗaya,” inji shugabar.
Ta ce jami’an hukumar ne tun da farko suka gano wajen, kuma ko da aka je, manajan da ke kula da wajen kawai aka tarar sai wani ma’aikacin wurin, inda aka kama su.
Ta kuma ce, “Ba mu da bayanan mamallakin wajen a matsayin dillalin waɗannan sinadaran da gwamnati ta san da zamansa. Mukan ajiye bayanan dukkan masu wannan harkar domin mu riƙa sa ido a kan shige da fice da kuma amfani da waɗannan sinadaran.
“Waɗannan sinadaran suna da matuƙar hatsarin da bai kamata a ce kowa kawai na ta’ammali da su ba. A ƙa’ida dole sai mutum ya samu izini daga Ofishin mai ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro kafin ya fara shigo da su da kuma izinin mallakarsu, wanda babu ɗaya daga cikin waɗannan da mamallakin wurin yake da shi.
“Ana buƙatar izinin ne saboda ana iya amfani da sinadaran wajen haɗa boma-bomai.
“Adadin sinadaran da muka gano a nan sun isa su tashi Kano gaba ɗaya idan aka yi wasa da su,” inji Mojisola.
Shugabar ta kuma ce yanzu haka suna ci gaba da titsiye mutanen da suka kama domin ganin an kama ainihin mamalakin wajen da ya riga ya cika wandonsa da iska don ya yi musu bayanin su wa yake sayar wa da sinadaran.
Sai dai ta ce za a bi hanyar da ta dace wajen lalata sinadaran bisa bin ƙa’idojin kiyaye lafiyar al’umma.
