Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamiɗo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano.

Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba.

Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana.

A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa.

Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi.

Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe maka zunubanka.” (Ko da yake Oshiomhole ya musanta yin wannan magana).

Lamido, ya gargaɗi gwamnati cewa amfani da ƙarfin iko wajen azabtar da ’yan adawa zai zama barazana ga dimokuraɗiyya.

Ya ce yanzu Nijeriya na fama da rashin tsaro, rarrabuwar kawuna da rashin amana, wanda shi ne abin da ya fi dacewa gwamnati ta mayar da hankali a kai.

Ya kuma soki yunƙurin da ake yi na kafa jam’iyyar haɗaka kafin zaɓen 2027.

Lamido, ya ce duk wani yunƙuri na kafa sabuwar ƙungiya ya zama wajibi ya dogara da manufofi masu amfani kamar dimokuraɗiyya, zaman lafiya, tsaro da cibgaban ƙasa, ba kawai burin mulki ko ramuwar gayya ba.

Duk da matsalolin da PDP ke fuskanta, Lamido, ya ce har yanzu yana da kishin jam’iyyar.

Amma ya ƙara da cewa, matuƙar PDP ba za ta samar da abin da ake so, zai mara wa wasu muddin hakan zai amfani ƙasa.

Game da zargin cewa yana yi wa jam’iyyar adawa aiki, Lamido ya ce: “Ina ƙoƙari ne na dawo da jam’iyyar PDP kan turbar da ta dace.”

Ya kuma zargi wasu gwamnonin PDP da yin aiki da Tinubu a ɓoye ba tare da an hukunta su ba.

Ya ce PDP sai ta dawo kan tsarin gaskiya, adalci da dimokuraɗiyya idan tana so ta dawo da ƙarfinta.

“ƙasar nan na cikin matsala ga yunwa, talauci, da rashin tsaro sun yawaita,” in ji shi.

Game da batun ƙirƙiro sabbin jihohi, Lamido, ya ce wannan ra’ayi yana da kyau amma ba yanzu ne lokacin da ya dace a bijiro da shi ba.

Ya ce ya fi dacewa a mayar da hankali kan warware matsaloli kamar rashin tsaro da yunwa.

Da aka tambaye shi game da ziyarar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai wa Shugaba Tinubu, Lamido, ya ce bai da abin cewa.

“Kwankwaso da Tinubu na da ‘yancin su gana. Ku tambaye shi da kanku,” in ji shi.

A ƙarshe, Lamido, ya ce mafitar Nijeriya na cikin dawo da amana, gaskiya, da bin doka a harkokin siyasa da gwamnati.

“Ina tare da PDP ɗari bisa ɗari, amma idan mafita ga Nijeriya tana wajen PDP, zan bi ta domin Nijeriya ta fi komai muhimmanci,” inji shi.

By ukarofi