An gudanar da bikin raba kyautuka ga haziƙan ɗaliban sakandaren gwamnati ta unguwar Gano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Dan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Kabiru ɗahiru Sule ADS ya yi alƙawarin gina wa makarantar sakandaren gwamnati ta Unguwar Gano masallaci da zauren jarrabawa a harabar makarantar kafin ƙarshen shekaran nan.

Ya bayyana hakan da yake jawabi a yayin taron ranar bayar da kyautuka da aka gudanar a harabar makarantar ranar Laraba bayan ya karɓi lambar yabo da makarantar ta karrama shi da ita. 

ɗan majalisar dai ya ƙara da ɗaukar nauyin biyawa ɗalibai masu hazaƙa guda 600 da za a sanya  a aji na musamman na makarantar, kuɗin rijista da za a zaɓo su daga gidajen masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya biya ba a yankin ƙaramar hukumar inda ya bada kuɗin N300,000 nan take tare da alƙawarin bayar da bencina na zaman ɗalibai guda 20 zai kuma yi ƙoƙarin kawo cibiyar yin jarrabawar JAMB a makarantar.

Ya ce ilimi shine ginshiƙin cigaban kowace al’umma da suke koyi da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf goyon baya a tsarin da ta ɗauka na sanya dokar ta ɓaci akan ilimi duba da ilimi na kowane za su yi ƙoƙarin taimakawa daidai da ikonsa.

Hon. Kabiru ɗahiru Sule ya bayyana irin ɗimbin ayyuka da ya gudanar a mazaɓun ƙaramar hukumar daban-daban kama daga gina rukunin ajijuwa da kuma gyaran makarantu da gina masallatai da cibiyoyin addinin Musulunci.

Shi ma a jawabinsa tun da farko shugaban makarantar sakandaren gwamnati na Unguwar Gano Malam Auwalu Ali Yalwa ya bayyana  taron da cewa shine na farko  na raba  kyautuka ga ɗalibai masu kwazo da aka yi a makarantar da ya  sami halartar ɗan majalisar  jiha  na  Tarauni Hon. Kabiru ɗahiru Sule da kansilan mazaɓar Unguwar Gano wanda shi ne ya wakilci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Hon. Ahmad Sekure Ita ma shugaban ƙungiyar shugabannin makarantun sakandare na jihar Kano Hajiya Uwani Ahmad Balarabe da mutane da dama sun halarta.

Ya ƙara da cewa zuwan sa a  matsayin shugaban makarantar ya sami kyakkyawan  haɗin kai daga malamai suna aiki tare don cigaban makarantar kuma shine ya bijiro da tsarin fara  yin Sallar Azahar a jam’i ga ɗalibai a makarantar. Sannan ya sama mata zama ɗaya daga cibiya ta yin jarrabawar WAEC da NECO da wasu makarantun ma za su zo su yi anan.

Shugaban makarantar sakandaren gwamnatin na Unguwar Gano ya ce yanzu suna da ƙarancin ajujuwa da rashin zauren jarabawa da kuma abin zama da masallaci wanda sun ji daɗin ɗan majalisar jiha da ya halarci  taron ya yi alƙawarin gina musu  sannan tsohon shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Habib Zakari shi ma ya yi alƙawarin kawo musu allo na zamani wanda wannan babban nasara ce a gare su suna kuma kira da azo a sama musu rijiyar burtsatse saboda sai sun fita wajen makarantar suke samun ruwa.

Malam Auwal Ali Yalwa  ya yaba da haɗin kai da iyaye suke basu ta yin  iya ƙoƙarinsu  musamman  ta yanda suke tiritiri da ‘ya’yansu wajen zuwa makarantar yana fata za su cigaba da juriya da bada kulawa sosai ya kuma nemi al’umma su cigaba da ba su haɗin kai.

A yayin taron makarantar sakandaren Gwamnatin ta Unguwar Gano ta karrama mutane  da dama da lambar yabo bisa gudummawa  da suke baiwa  bunƙasa cigaban ilimi ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Tarauni da Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ɗan majalisar jiha da shugabar ƙungiyar ANCOPSS ta jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da malaman makarantar masu haɗaƙa.

By ukarofi