Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi a 2023, ya bayyana cewa zai goyi bayan Obi, idan har yana da niyyar sake tsayawa takara a 2027, ko da kuwa ba tare da shi ba.
Peter Obi da Datti sun tsaya takara tare a 2023 sai dai sun ƙare a na uku.
Shugaba Bola Tinubu ne ya lashe zaɓen.
Datti, ya ce Obi yana da ’yancin sake tsayawa takara a ƙarƙashin LP.
Ya kuma ce ba dole ne sai Obi ya yi haɗin gwiwa da shi ba.
“Peter Obi mutum ne da nake girmamawa ƙwarai. Yana da damar sake fitowa takara a 2027, ko da ba tare da ni ba,” inji Datti a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
Datti, tsohon Sanata ne, ya ce Nijeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya da za su iya kawo ci gaba, ba masu alƙawuran ƙarya ba.
“Muna cikin wani yanayi mai muhimmanci. ’Yan Nijeriya na buƙatar aiki ba uzuri ba. Muna buƙatar shugabanni masu cika alƙawari da gyara ƙasa,” inji shi.
Game da shigar Peter Obi a wata haɗakar siyasa a jam’iyyar ADC, Datti ya ce hakan ba laifi ba ne.
“Haɗin gwiwa a siyasa ba cin amanar jam’iyya ba ne. Hakan al’ada ce a siyasa, inda mutane da jam’iyyu ke haɗuwa don cimma buri ɗaya.
“Ni ma na halarci wasu daga cikin tarukan. Ba wani abu ba ne da ya saɓa wa doka ko tsarin jam’iyya,” inji shi.
