Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta kama mutane 6 tare da rufe shaguna da dama a kasuwar Sabon Gari da ke Kano saboda sayar da mayukan shafawa na bilicin.
Ko’odinetan hukumar a Kano, Kasim Ibrahim, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce, wannan samame na zuwa ne bayan samun ƙorafi da suka yi ta dandalin sada zumunta da kuma umarnin ɗaukar mataki daga darakta-janar na hukumar.
“Bayan samun ƙorafi da muka yi a shafukan sada zumuntarmu daban-daban da kuma umarnin daga darakta-janar, shi ne muka gudanar da sa-ido na sirri da gano shagunan da suke sayar da waɗannan mayuka,” a cewar Ibrahim.
Ya ƙara da cewa binciken hukumar ya gano mutane 6 da ake zargi da hannu wajen rarraba kayayyakin bilicin ba tare da wani kyakkyawan tsari ba.
“Hukumar ta kuma ce ana kasuwanci mayukan ne da sunan na gyaran jiki, amma da suke ɗauke da sinadarai da hukumar ba ta amince da su ba.”
“Bayan gudanar da zuzzurfan bincike, mun gano mutane shida da suke da hannu wajen raba haramtattun mayukan,” Ibrahim ya faɗa.
Ibrahim ya ƙara da cewan sun rufe wasu shaguna da mayukan shafe-shafe na bogi ko kuma amfani da rajistar NAFDC ta ƙarya.
NAFDAC ta jaddada aniyarta ta cigaba da bibiya da sa ido kan kayayyaki da ake samarwa da rarraba su da sayar da su da suka hada da mayuka shafawa domin kare rayukan al’umma.
Ya buƙaci ‘yan Nijeriya za su zama masu lura da ba da rahoton ga hukumar a ƙarƙashin jagorancin Mojisola Adeyeye.
Daga nan ne Ibrahim ya yaba wa kafafen yaɗa labarai kan yadda suke tallafa wa ayyukansu da jaddada musu yadda hukumar ta himmatu wajen kiyaye lafiyar ‘yan Nijeriya.
