Shugaban ƙaramar hukuma ya yaba wa Gwamna Inuwa kan samar da romon dimukraɗiyya a Gombe

Spread the love

Daga GAMBO ISA

Shugaban ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, Honorabul Abubakar Hassan Diffa ya yaba wa gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya bisa ci gaban da yake samarwa a jihar.

A cikin wata sanarwa da ta raba wa jaridun Blueprint a Abuja, shugaban ƙaramar hukumar ya zayyana nasarorin da gwamnan ya samu a fannin bunƙasa rayuwar bil’adama, shirin noma da kiwo, ilimi, cibiyoyin kiwon lafiya, gina ingantattun abubuwa na zamani, sakatariyar ƙaramar hukuma a wasu ƙananan hukumomin, asibiti a Yamaltu Deba, hanyoyin cikin gari da sauransu.

Diffa ya yaba wa gwamnan kan gina katafaren fada a masarautun Daɗin Kowa da Deba da kuma samar da cibiyar masana’antu a ƙaramar hukumar Yamaltu Deba.

Shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya zayyana wasu nasarorin, ya ce: “Ayyukan da suka shafi jama’a kamar gina babban asibitin Yamaltu Deba na zamani, sakatariyar kansilolin yankin, gina tituna a garuruwan Kuri, Dassa, Lambam, Tsando, Balanga Maio da sauran ƙananan hukumomin jihar sun yi matuƙar tasiri ga rayuwar al’umma.

“Gwamna Yahaya ya bada muhimmanci ga gina rayuwar marasa galihu da marasa ƙarfi, ya fitar da shirye-shiryen ɗaukar ma’aikata da dama, inda sama da malamai 10,100 a majalisar suka amfana.

“Me za a ce game da gina manyan makarantu a ƙaramar hukumar Yamaltu Deba da ke yankin Daɗin Kowa da sauran gundumomi, horar da likitoci, ma’aikatan jinya, ungozoma, gine-ginen cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ɗakunan shan magani a gundumomin ƙaramar hukumar Yamaltu Deba da kansilolin yankin goma sha ɗaya, a jihar domin samar da ingantaccen kiwon lafiya.”

Yayin da yake kira ga ‘yan ƙasa, musamman matasa da su mayar da martani ga wannan matakin na gwamna, shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da umartarsu da su bi dokokin tsarin mulki, da gujewa shan ƙwayoyi, rungumar sana’o’i domin dogaro da kai.

Daga nan Diffa ya ba da tabbacin a shirye yake ya yi aiki tare da gwamnan domin ganin an samu ribar dimokuraɗiyya a jihar.

By ukarofi