An buƙaci amfani da ilimi wajen sauya tunanin matan da Boko Haram ta ci zarafinsu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Asusun tallafawa mutanen da hare-haren ’yan ta’adda ya shafa na duniya, tare da haɗin gwiwar Gidauniyar NEEM da ke bayar da agaji ga al’ummomin da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita, sun buƙaci gwamnati da al’umma da su yi amfani da ilimi a matsayin hanya ta sauya tunanin mata da ’yan mata da mayakan Boko Haram suka ci zarafi tsawon shekaru a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

A wani taron da suka gudanar a birnin Abuja, sun bayyana cewa sama da mutane miliyan ɗaya da rikicin ya shafa sun amfana daga shirye-shiryensu na tallafi, ciki har da wasu daga cikin matan da aka ci zarafi da ke bayyana irin ci gaban da suka samu.

Hare-haren ƙungiyoyin ’yan ta’adda irinsu Boko Haram a Arewa maso gabashin Nijeriya ne ya sa waɗannan ƙungiyoyi samar da shirye-shiryen da ke tallafa wa ’yan mata da mata da aka ci zarafi.

Shugabar asusun tallafa wa mutanen da hare-haren ’yan ta’adda ya shafa na duniya a Nijeriya Madina Malefakis, ta bayyana maƙasudin da ya sanya suka shirya taron.

”Muna ƙoƙarin tallafa wa mata ko ‘yan matan da Boko Haram ta ci zarafinsu, ta hanyar komawa makaranta don ci gaba da karatu domin inganta rayuwarsu”, inji ta.

A nata jawabi, shugabar Gidauniyar NEEM, Fatima Aƙilu, ta ce kusan mutum miliyan ɗaya ne suka amfana daga shirye shiryensu da suka shafi gyaran rayuwa da tunani ya hanyar ilimantarwa.

ɗaya daga cikin matan da rikicin Boko Haram ya shafa, ta ce za ta jima ba ta manta uƙubar da ta shiga ba sakamakon ayyukan mayaƙan Boko Haram, bayan da suka kamata a baya kuma suka ci zarafinta.

By ukarofi