
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta amince da kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su gudanar da jigilar mahajjatan ƙasar yayin harkokin aikin Hajjin shekarar 2027.
NAHCON ta sanar da haka ne wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis. Ta ce, kamfanonin da aka amince da su sun haɗa da Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Aviation Services Limited.
A cewarta, an zaɓi kamfanonin ne bayan tantance su da kwamitin tantance kamfanonin jiragen sama ya gudanar, bisa la’akari da ƙa’idojin tsaro, ƙarfin matakin gudanar da aiki da kuma yanayin harkokin kuɗaɗen hidima.
Haka kuma, ta ce amincewar ta dogara ne da kammala yarjejeniyar jigilar maniyyata tsakaninta da su tare da cika dukkan sharuɗɗan hukumomin kula da sufurin jiragen na Nijer da na Saudiyya na aikin Hajjin 2027.
Kazalika, ta ce za a tsara rabon maniyyata da jaddawalin zirga-zirgar jiragen sama tare da hukumomin walwalar alhazai na jihohi da kuma kamfanonin jiragen da al’amarin ya shafa.
Har ila yau, NAHCON ta kuma gargaɗi kamfanonin da su tabbatar da bin sharuɗɗa da ƙa’idojin aikin Hajjin 2027, ciki har da bayar da tikitin jirgi mai alaƙa da bayanan maniyyata na Nusuk-Masar, da kuma kiyaye dukkan ƙa’idojin tsaro a lokacin.
NAHCON ta bayyana cewa wajibi ne kowane mahajjaci ya samu damar ɗaukar akwati guda mai nauyin kilogram 32 da kayan hannu mai nauyin kilogram 8 bisa sharuɗɗan hukumomin kula da harkokin jiragen sama.
A ƙarshe, hukumar ta kirayi dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa kai da kamfanonin domin tabbatar da jigilar maniyyatan Nijeriya cikin sauƙi, tsaro da kuma walwalar ibadar.
