Daga USMAN KAROFI
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fara rarraba muhimman kayan zaɓe zuwa ƙananan hukumomi 30 na Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa ranar Asabar, 15 ga Agusta 2026. Kwamishinan INEC mai kula da zaɓen Osun, Kunle Ajayi, ya bayyana cewa ana gudanar da rabon kayan ne daga ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Osogbo, babban birnin jihar.
Ajayi ya ce an samu jinkirin rarraba kayan zaɓen ne sakamakon jinkirin isowar sabbin takardun kaɗa ƙuri’a da sauran kayan zaɓe daga Abuja. Ya bayyana cewa an sake buga takardun ne bayan da aka shigar da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) cikin jerin jam’iyyun da za su fafata a zaɓen. Hakan ya sa INEC ta sake daidaita takardun kaɗa ƙuri’a da na sakamakon zaɓe domin su dace da sabon jerin ‘yan takarar.
Shigar da ɗan takarar SDP, Francis Ajala, da mataimakinsa Faseke Oladipo, ya ƙara yawan jam’iyyun da za su fafata a zaben zuwa 15. INEC ta ce za a tabbatar da isar da sabbin kayan zaɓen zuwa dukkan wuraren da aka ware kafin fara kaɗa ƙuri’a. Hukumar ta kuma yi kira ga jam’iyyu, ‘yan takara, jami’an tsaro da masu kaɗa ƙuri’a da su haɗa kai wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.
